Jami’an ’Yan Sanda 2,000 Aka Tura Nasarawa Don Shagulgulan Sallah Lafiya

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Nasarawa, Mista Bola Longe ya ce, rundunarsa ta tura jamiíanta 2000 a dukkanin sassan Jihar domin tabbatar da anyi shagulgulan Sallah lami lafiya. Ya shaidawa wakilinmu cewa, “Rundunarmu ta samar da cikakken tsaro domin ganin anyi bukukuwan Sallah ba tare da samun wani hargitsi ba, ta hanyar tura jamiíamu cikin fararen kaya a dukkanin lunguna da sako na sassan Jihar domin su sanya ido su kuma rika kawo mana rahotannin sirri a kan duk abubuwan da suke gudana. Mun kuma sanya jamiían namu masu yawa suna kai komo a kan manyan titunan Jihar namu domin tabbatar da tsaro ga matafiya.”

A cewar shi, rundunar ta sanya jamiían nata a dukkanin filayen da za a gudanar da Sallar Idi da kuma wuraren shakatawa domin su bayar da tsaron da ya kamata. Mista Longe, ya yi kira ga alíummar Jihar da su sanya ido sosai a lokacin bukukuwan Sallah da ma bayan nan, su kuma hanzarta kiran wadannan lambobin wayan, 08108795930 and 08112692680, a duk lokacin da suka hangi wani abin da ba su fahimce shi ba.

Exit mobile version