Jami’an ‘Yan Sandan Da Aka Sace Sun Kubuta

Rahotanni daga jihar Zamfara sun tabbatar da cewa jami’an ‘yan sandan nan da aka sace tsakanin Zamfara da Katsina da ke arewa maso yammacin Nijeriya sun kubuta. Wasu majiyoyi sun shaida cewa ‘yan bindigar sun saki ‘yan sanda biyar da suka sace bayan da takwas daga cikinsu suka tsere.

An kwantar da ‘yan sandan biyar a wani asibiti da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara inda ake duba lafiyarsu. Tun da farko an tabbatar da cewa ‘yan sanda su 12 masu mukamin ASP ne ‘yan bindigar suka sace a wani kauye da ke tsakanin jihohin Katsina da Zamfara.

Sai dai wasu manyan majiyoyi daga gwamnatin jihar ta Zamfara sun tabbatar cewa daga cikinsu sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen inda suka bar biyar a hannunsu.

“Wani shugaban ‘yan bindiga da ya sa aka sace su ne ya mika su bisa fahimtar juna ba tare da an bayar da kudin fansa ba. Yanzu haka suna hannun Kwamishinan ‘yan sanda na Zamfara,” in ji wata majiyar.

Sai dai wata majiya ta daban ta ambato daya daga cikin ‘yan sandan yana cewa sai da ya biya kudin fansa kafin a sake shi.

Exit mobile version