Connect with us

NOMA

Jamiar Ahmadu Bello Ta Bayar Da Gudummawar Habaka Ilimin Noma kasar nan.. Farafesa Garki

Published

on

Assalamu alaikum, ranka ya dade masu karatu za su so su san sunanka da matsayinka a yanzu.

 

Sunana Farfesa Shehu Ado Garki, kuma matsayina yanzu shi ne ni shugaban jami’ar Musulunci ta farko a Nijeriya wato Al-kalam Unibersity tun kusan biyar da suka wuce.

 

Kasantuwarka tsohon malami wanda ya ga jiya, ya ga yau a jami’ar Ahmadu Bello, yanzu kuma ga ka shugaban jami’a a wannan wuri, ko za ka gaya wa jama’a wani abu da ka tsotsa daga jami’ar Ahmadu Bello wanda kake tunanin zai iya amfanar jama’a nan gaba?

 

To wallahi kasancewa ta na dade ina aiki a jami’ar Ahmadu Bello kafin na fara aiki a wannan jami’a ta Musulunci ta Al-kalam da take a Katsina, hakika na amfana da abubuwan da na koya a lokacin da na yi aiki a jami’ar Ahmadu Bello. Tun farko dai ni dalibi ne a jami’ar Ahmadu Bello, tunda na gama sakandire na shigo jami’ar Ahmadu Bello, na yi makarantar share fagen shiga jami’a wato School of Basic Studies a shekara ta 1975 zuwa da 1976 daga nan na shiga tsangayar koyon aikin noma na zamani, wato Faculty of Agriculture daga 1976, sai kuma a 1979, na je hidimar kasa jihar Legas na je na koyar da fannin noman zamani a wata karamar sakandire daga nan da na dawo na fara aiki a jihar Kano na dan lokaci kadan sai jami’ar Ahmadu Bello in muna bukatar mu yi aiki da jami’ar za su ba mu aiki. Muka zo aka yi mana interbiew na fara aiki, to tun daga nan na fara aiki sai kuma na ci gaba da karatun digiri na biyu a fannin yadda za a kirkiro sabbin iri, to da na kammala a 1983 sai kuma na ci gaba da karatun digiri na uku, wanda ake kira PhD to shi wannan digiri na ukun shi ne na kammala a 1991 to bayan na gama digiri na na uku ban jima ba lokacin da aka kirkiro jihar Jigawa daga jihar Kano. Sai jihar Jigawa suka ce za su kafa makarantar koyar da ayyukan gona wato College of Agriculture a Hadeja to shi ma ina gida suka zo suka roki in karbi wannan makaranta, to na amsa masu na je na yi shekara biyar a Hadeja, daga nan kuma na dawo, da na dawo Zariya na ci gaba da ayyukan bincikena na ayyukan gona ba jimawa aka ba ni Head of Department wato na nan Department of Plant Science, na yi aikin shekara biyu da rabi a matsayin shugaba a nan gurin, daga nan kuma ba jimawa sai aka ba ni Deputy Director na Institute for Agricultural Research, wato mukaddashin shugaban wannan ma’aikata mai dumbin tarihi ta bincken aikin noma wadda ta ke a nan Samaru Zariya. Aka ba ni Deputy Director na yi shekara biyu, bayan na gama shekara biyu sai kuma aka bani na zama cikakken Director na shugabancin gurin baki daya na shekara hudu, to dama shekara biyu-biyu ake bayarwa sau biyu, idan an kammala shekara hudu sai kuma a ba wani, to bayan na gama wannan shekara hudun shike nan na dawo na ci gaba da aikina da na saba na bincike sai aka same mu kuma da cewa an kafa jami’ar Musulunci ana neman shugaba, wato ana neman bice Chancellor kuma ana so ni in je in karbi wannan aiki, to da fari dai na nuna masu alamar ba zan so a ce ni zani ba, amma dai su mutanen suka ce in je, to Alhamdu lillahi na karba dai na je, to yanzu dai a nan jami’a shekara ta ta biyar ke nan, to kuma dama a kan bada shekara biyar ne a yi wannan matsayi na bice Chancellor kodayake a matsayin jami’ar da ba ta gwamnati ba wata kila ya yiwu a ba da damar kari inda bukatar haka. To kamar yadda ka tambaye ni, shin zamana a jami’ar Ahmadu Bello yana da tasiri ko alaka da aikin da nake yi yanzu? To a gaskiya abu ne wanda yake da tasirin gaske saboda kasnce wa ta, ka dai ji yadda na taso, komai da ma a Zariya, tun daga karatu kafin in yi digiri, da digiri na daya da na biyu da na uku duk a Zariya na yi su, saboda haka ni yadda ake gudanar da mulki ko kuma tafiyar da ayyukan yau da kullum a jami’ar Ahmadu Bello abu ne da yake sannane gareni, tunda duk wadannan shekarun da muka yi a ciki ya ba mu damar mu ga me ake yi kuma ya ake yi. Wannan gaskiya shi ne abin da ya taimake ni ba dan kadan ba da na je a matsayin shugaban jami’a ta Al-kalam wadda take sabuwar jami’a ce. Wadda da na je ban jima ba na bi irin ka’idojin da na koya na tafi da shugabanci a jami’a, Allah da ikonsa muna yi, mun samu ana karantar da fannoni 4 ne kawai a jami’a a lokacin da muka je amma yanzu cikin ikon Allah mun samu karin fannoni 18, ya yadda a yanzu maganar da muke a wannan jami’a fannonin digirin da ake bayarwa sun kai ashirin da biyu, kuma bacin haka mun kai matsayin yanzu mun fara karantar da digiri na biyu a wasu daga cikin fannonin, saboda haka a lokacin da na je, daliban makarantar duka ba su fi 260 ba, amma yanzu maganar da ake dalibai a makarantar sun wuce 8,000.  To wannan shi ne daya daga cikin abubuwan da zan ce zamana da kuma aikin da na yi a jami’ar Ahmadu Bello ya taimaka min wajen tafiyar da sabon wurin aikin nawa da na je na samu na wannan sabuwar jami’a, kodayake kamar yadda na ce da na yi shugabancin College of Agriculture to amma ita College of Agriculture ba ta kai darajar jami’a ba, saboda haka abin da na koya a can shima ya taimaka mini amma dai ba kamar abubuwan da na koya a nan jami’ar Ahmadu Bello suka taimaka mani ba.

 

Wane tasiri kake ganin jami’ar Ahmadu Bello a rayuwarka?

 

Jami’ar Ahmadu Bello ai ita uwa ce, kuma kamar yadda muke fada wannan jami’a ta Ahmadu Bello ai ta karantar da mutane da yawa, har shugaban kasa an samu daga wannan jami’a, Allah ya jikan Umaru Musa ‘Yar Adua, dalibin Ahmadu Bello Unibersity ne. An sami gwamnoni daga Arewa daga Kudu wadanda daga nan jami’ar suka yi karatu an sami manya-manyan mutane a kasa ballantana kuma ma’aikata irin mu wadanda aka ba su shugabancin jami’o’i wato bice Chancellor a yanzu haka a Committee of bice Chancellors da muke da shi in muka je na fara kirgawa mutanen da daga jami’ar Ahmadu Bello ne suka zama suna nan da yawa, saboda haka jami’ar Ahmadu Bello kam alhamdulillahi jami’a ce mai albarka wadda kuma ta yi fice ba wai kawai a Nijeriya kadai ba a duk duniya.

 

A karshe ranka ya dade wane kira za ka yi wa ‘yan baya?

 

 

‘Yan baya abin da za a yi kira gare su shi ne su mai da hankali ga koyon abin da suka zo koya musamman dalibai, su kuma ma’aikata su ma su mai da hankali ga koyon aikin yadda ya kamata, su kasance suna yin abubuwan gwargwadon yadda ya kamata. Akan ce karatu da aiki da sauransu sun tabarbare to amma idan mutane suka mai da kai to insha Allahu za su koyi abubuwan da suka kamata su koya kuma in dai sun mai da kai za su yi aikinsu yadda ya kamata su yi, to wannan shi ne zan kira mutane da dalibai na baya da kuma su ma ma’aikatan na baya su kasance suna yin biyayya kuma suna yin aikin yadda ya kamata. In karatu suka zo yi su tabbata karatu za su yi ba shiririta, su raba kansu da irin wadannan abubuwa da ake yi musamman na shaye-shayen kayan maye da aka ce ya addabi mutanen Arewa da sauransu.

 

 

 
Advertisement

labarai