Hukumar gudanarwa ta jami’ar Bayero, ta amince da soke zangon karatu na shekarar 2019/2020 da dalibai suka fara. Hukumar ta bayyana ranar 18 ga watan Janairun 2020 a matsayin ranar komawar dalibai.
Amma wannan sokewar ba ta shafi masu karatun digiri na biyu da na uku wurin biyan kudin makaranta ba, wannan na kunshe ne a wata takarda da rijistirar makarantar, Fatima Binta-Mohammed ta sanya wa hannu.
Kamar yadda takardar ta bayyana, dalibai masu digirin farko, za su fara zangon karatunsu ne a ranar 18 ga watan Janairu yayin da sashi na biyu na zangon karatunsu zai fara a ranar 3 ga watan Mayun shekarar 2021.
Hukumar gudanarwar ta bayyana ranar 18 ga watan Janairu da zama ranar farko da masu digiri na biyu da na uku, zasu fara sashin karatu na farko inda sashi na biyu zai fara a 1 ga watan Yuni.