Jami’ar BUK Ta Kori Dalibai 63 Bisa Aikata Laifuka

Jami’ar Bayero dake Kano wato BUK ta kori dalibai 63 tare da dakatar da guda 13 bisa samun su da aikata laifuka daban-daban wanda ya hada da na satar jarabawa da rashin  da’a.

Wannan bayanin ya fito ne a takardar da Daraktar shirya jarabawa, bayar da takardar gurbin karatu da kuma tattarawa a jami’ar, Amina Umar-Abdullahi ta fitarwa da manema labarai a Kano a ranar Juma’a.

A cewarta wannan matakin an dauka ne bayan da kwamitin jami’ar mai lura da jarabawa da kuma rashin da’a ya amince da hakan a ranar Larabar 28 ga watan Agustan 2019 a zaman jami’ar na 374.

Ta tabbatar da cewa daliban da aka kora sun hada guda 10 daga makarantar masu karatun digiri na biyu zuwa sama, da kuma guda 10 daga sashen SCE, tare da bakwai daga daga tsangayar lura da kimiyyar lafiya da kwamfuta.

Sauran sun hada da wadanda suka fito daga tsangayar ilmi, kimiyya, da bangaren Injiniya da FESS da sauran su.

Haka zalika bangaren fasaha da kuma ilimin addinin Musulunci, da na sadarwa da sauran su.

 

Exit mobile version