Khalid Idris Doya" />

Jami’ar FUTA Ta Tabbatar Da Kisan Da Aka Yi Wa Mataimakin Rijistanta

Jami’ar kimiyya ta gwamnatin tarayya da ke Akure (FUTA) ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin mataimakin Rijistanta, Dakta Amos Arijesuyo, wanda shi ne shugaban sashin kula da ladaftarwa da horas da dalibai wanda ya mutu sakamakon raunukan da ya samu na harbin bindiga yayin da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai masa hari a cikin motarsa yayin da ke tafiya a kan hanyar Ilesa zuwa Akure da yammacin ranar Asabar 16 ga watan Janairun nan.

Mataimakin Daraktan sadarwa na jami’ar FUTA, Mista Adegbenro Adebanjo, ya shaida hakan ne a cikin sanarwar da ya rabar wa ‘yan jarida shekaran jiya.

A cewarsa, Adebanjo, shi marigayi Arijesuyo wanda ke dawowa zuwa Akure daga tafiyar da ya yi zuwa Ibadan ne wasu ‘yan bindiga suka tareshi tare da jan motarsa zuwa daji wajajen karfe biyar na yammacin ranar.

Ya ce, “Yan bindigan sun yi harbe-harbe wa motar.

“Abun takaici, wasu daga cikin harsasan sun samu Dakta Amos Arijesuyo shi da direbansa. Duk da harbin da aka musu, direban ya yi kokarin jawo motar domin arcewa daga inda lamarin ya faru da kokarin kai su ga wani asibiti da ke kusa.

“Shi Daktan ya gamu da raunuka sosai wanda hakan ya janyo rasa ransa, shi kuma direban na amsar kulawar likitoci a asibiti.

“Jami’ar nan tana tir da Allah wadai da wannan aika-aikan rashin hankali, dabbanci da hauka da wasu jahilai suka aikata na kashe hazikin malamin jami’a wanda hakan babban rashi ne ga ci gaban.

“Mutuwar Dakta Arijesuyo babban rashine ga jami’ar FUTA da ma bangaren ilimi gaba daya a Nijeriya.

“Muna fatan za a tabbatar da kamo wadanda suka aikata wannan aika-aikatar tare da gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar shari’a daidai da laifukansu.”

Jami’in yayi fatan iyalan marigayin za su yi jure wannan babban rashin da suka yi gaba daya, yana mai cewa tabbas sun ji zafi matuka bisa rashinsa.

 

Exit mobile version