Jami'ar Gusau Ta Kori Dalibai 7 Ta Dakatar Da Karatun 6 Kan Rashin Da'a
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’ar Gusau Ta Kori Dalibai 7 Ta Dakatar Da Karatun 6 Kan Rashin Da’a

byKhalid Idris Doya
2 years ago
Jami'ar Gusau

Jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ta dauki mataki mai tsauri na ladabtar da dalibai 13 ciki har da mata uku da aka samu da laifuka daban-daban da suka kunshi sata, coge don samun damar karatu, satar jarabawa da sauransu.

A sanarwar manema labarai da jami’in watsa labarai na jami’ar Malam Umar Usman ya fitar, ya ce, laifukan da aka samu daliban da aikatawa sun saba wa sashin doka A item (xxv) shafi na 62, da shafi 68 item (iv) na kundin tsare-tsare da dokokin da ke tafiyar da da’ar dalibai, tare da sashi L shafi 69-73 item (i-xxv) na kundin littafin dalibai.

  • Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Sayar Da Hannun Jarin Wasu Tashoshin Jiragen Sama

Ya ce: “Hukumar gudanarwar jami’ar a zamanta karo na 82 da ya gudana a ranar 5 ga watan Yulin 2023 ta yi nazari da la’akari da shawarorin da rahoton kwamitin ladabtar da dalibai (SDC) ya bayar na kokar dalibai bakwai da dakatarwa/tsawaita wa’adin karatun dalibai 6 bisa samun su da laifukan rashin da’a.

“Daliban da lamarin ya shafa sun aikata laifukan da suka saba wa dokokin da ke tafiyar da harkokin dalibai na jami’ar,” ya shaida.

Ya kuma ce dauka da tabbatar da wannan matakin ya fito ne daga wajen mai rikon sakataren ilimi na jami’ar, Malam Mu’awiyya Bello a madadin rijista Malam Yakubu Audu Anivbassa da ya fitar a ranar 7 ga Yuli.

Daliban da wannan matakin na korar ya shafa sun hada da Daniel Ibeh Mayowa, Habibu Abdul, Abdulsalam Abubakar, Faruk Alayande Olamilekam, Iortim Philemon Vasue, Abubakar M. Usman tare da James Joseph.

Sannan wadanda kuma aka Dakatar da karatunsu na wasu lokuta daga zangon karatu daya wasu zangon karatu biyu; Emmanuel Chibuzor Ejikeme, Idowu Ojo Oni, Khadija Abdulrahman Bala, Sadiya Sani Garba, Balkisu Bello da kuma Ibrahim Mu’azu Lawal.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Next Post
NATO Har Tana Son Sa Hannu Cikin Harkokin Yankin Asiya Da Pasifik

NATO Har Tana Son Sa Hannu Cikin Harkokin Yankin Asiya Da Pasifik

LABARAI MASU NASABA

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version