Daga Muhammad A. Abubakar
Kungiyar Malaman Jami’o’i wato ASUU ta bayyana Jami’ar Ilorin a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda sakamakon sauke shugaban kungiyar ta ASUU shiyyar Ilorin Dakta Kayode Afolayan da Jami’ar ta yi bisa zargin yadda ya fallasa cin hanci da rashawar da Shugaban Jami’ar Farfesa Abdulganiyu Ambali (mai baring ado) ya tafka.
A wata wasika da Ciyaman na kungiyar ASUU reshen Jami’ar Ibadan, Dakta Ayodeji Omole ya sakawa hannu a madadin kungiyar da kuma Kodinetan Shiyyar na kungiyar ASUU, Dakta Ade Adejumo, Malaman sun bayyana cewa; Jami’ar Ilorin a karkashin Ambali ya aikata wasu laifuka na kuntata wa tare da takura wa wasu ayyuka da ake yi bisa doka domin yadda yake tsoron fallasa mugun ayyukan da ya aikata a Jami’ar.
Kamar yadda aka bayyana a wasikar; “Tabbas, Jami’ar tana alfahari da yadda take son kashe wasu dalibai da Malamai wadanda suke da alaka ta kusa ko ta nesa da shugabancin kungiyar ASUU. Wannan laifi na kiyayya a bangaren Jami’ar ana aikata su ne da sunan gyaran kalandar makarantar. Duk da da yawan Jami’o’i suna tabbatar da sun tsaida tsayayyen kalandarsu ba tare da sun lalata membobin kungiya ko ayyukansu ba. Koma da wacce manufar aka yi, Jami’ar Ilorin ta zama kungiyar ‘yan ta’adda lura da zamantakewarta da ma’aikatu.”
Takardar ta ci gaba da cewa; “Shugaban Shiyyarmu, Dakta Afolayan a madadin kungiyar ASUU, ya sakawa wata wasika hannu yana mai nusar da hukumar Jami’ar da su duba hawan kawarar da Farfesa Ambali ya ke yiwa tsari da dokokin Jami’ar. Maimaikon su duba hobbasan da ya yi da gudanar da bincike, sai Shugaban Jami’ar mai baring ado ya aika wa da Afolayan takardar gargadi bisa zarginsa da yamadidi da wata takarda akan Shugaban Jami’ar.”
Sannan takardar ta kara da cewa; “A ranar 21 ga watan Satumban 2017, hukumomin Jami’ar suka kammala aikinsu na rashin bin doka, take hakki da ‘yanci da rashin bin ka’ida suka soke takardar aikin Afolayan.”
Kungiyar ASUU ta yi zargin cewa; duk da korafi da suka shigar ga Hukumomin EFCC da ICPC da sauran hukumomi masu bincike kan yaki da cin hanci da rashawa, amma har yanzu ba a fitar da sakamakon binciken ga al’umma ba.
Inda suka ce; “akwai matukar damuwa na yadda Jami’ar Ilorin ta kulla alaka ta sirri da wasu hukumomi domin boye abubuwan da suka aikata. Misali; kungiyarmu, ta shigar da korafi a watan Disamban 2016 ga Hukumomin EFCC, ICPC da CCB, amma har yanzu sakamakon binciken ba a bayyanawa al’umma ba. Kuma kungiyarmu ta rubuta korafi ga Ma’aikatar hukumar Ilimi da masu ziyartar makarantar, amma har yanzu babu wani kwakkwaran mataki da aka dauka. Shirun wadannan hukumomi da kuma halin ko-in-kula da gwamnati ta nuna, ya saka mana shakkun akan shirin yaki da cin hanci da rashawa.” Inji takardar.