Muazu Hardawa" />

Jami’ar Noun Na Daukar Dalibai Kowane Lokaci A Bauchi – Farfesa Muhammad

Jami’ar karatu daga nesa ta kasa wato Open Unibersity reshen Bauchi ta ja hankalin matasa da ma’aikata su himmatu wajen shiga jami’ar don yin nazari kan fannoni dabam dabam da suke bukata a duk lokacin da suke so ko suka samu dama domin samun takardun shaidar ilmin jami’a masu inganci kamar yadda ake samu daga kowace irin jami’a da ake da ita a kasar nan.

Farfesa Mohammed Abdullahi Bello shugaban jami’ar karatu daga nesa NOUN ya bayyana cikin hirar sad a wakilin mu a ofishin sa da ke Bauchi, inda ya kara da cewa wannan jami’a ta Open Unibersity tana kara inganta ayyukan ta wajen ganin kowane mutum ya samu shiga ya karanta darasin da ya ke so a lokacin da ya ke bukata. Saboda suna daukar ma’aikatan gwamnati da ke son karatu a kowane lokaci da kuma samarin da suka rasa guraba a sauran jami’o’in da ake karatu a ciki saboda yadda dalibai ke bukatar guraba. Don haka kowane mutum zai iya shiga Open Unibersity ba tare da yayi jarrabawar JAMB ba, kuma zai iya shiga a kowane lokaci yake bukata ya kuma kammala a lokacin da ya ke so.

Ya kara da cewa basu da lokacin daukar dalibai ko lokacin kammalawa sai lokacin da mutum ya ke son ya shiga sai ya sayi takardar cikewa ya cika ta yanar gizo da takardun karatun sa, musamman wadanda ke da ilmin Difloma ko wadanda suka jima suna aikin gwamnati amma suna son yin digiri ko babban digiri ko digirin digirgir. Don haka ya bayyana cewa a Bauchi suna da dalibai sama da dubu biyar amma a kudancin Nijeriya kamar Jihar Lagos da sauran Jihohi ana samun dalibai dubu 20 zuwa 30 a jiha daya tak, kuma suna karatu suna kammalawa a duk lokacin da suke bukata shi ne banbanci da sauran jami’o’i da ke karatu cikin shekaru uku ko hudu su kammala.

Exit mobile version