Jami’ar NOUN Ta Amince Da Sabbin Darussa 15

Hukumar zartarwa na Budaddiyar Jami’ar Nijeriya wato NOUN ta amince da sabbin darussa goma sha biyar a matakin digirn farko da na biyu domin bai wa ‘yan Nijeriya damar karantar wadannan darussa a cikin Jami’ar.

Farfesa Peter Okebukola, shugaban hukumar zartarwar Jami’ar, shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Ya tabbatar da cewa; uku daga cikin darussan an amince da su ne a matakin digiri na farko. Darussan kuwa sune; huldar jakadanci (International Relations), harshen Faransanci (French), da kuma Ilimin kawo ci gaba (Development Studies).

Okebukola ya ci gaba da cewa; darussa 12 kuwa an amince da su ne a matakin digiri na biyu da na uku.

Darussan kuwa sun hada da; Digiri na biyu kan Lauya, da kuma Kan Huldar Jakadanci, da sha’anin lafiyar al’umma da tsimi da tanadi, tare da ilimin sadarwa.

Sauran sun hada da; Ilimin ‘Cyber Security,’  ‘Artificial Intelligence’ da kuma ‘Management Information System.’

Ya kara da cewa; Jami’ar tana fatan ta cimma burinta na ilmantar da dalibai miliyan guda idan aka yi duba da wadanda suke karatu a jami’ar na adadin da ya kai 550,000.

Exit mobile version