A kalla mutane goma sha uku har da wata jami’ar soja suka rasa rayukansu a lokacin da mummunan hadari ya rutsa da su a daidai yankin Emohua da ke Yamma maso Arewa a kan gadar Choba a cikin jihar Ribas.
Hadarin ya auku ne lokacin da motar Bas kirar Hiace take dauike da fasinja guda goma sha hudu a cikinta, inda ta yi taho mu gama da wata motar kirar pail loader.
An ruwaito cewa, fasinjojin da suke cikin motar, suna kan hanayarsu ce ta zuwa jihar Legas a ranar Alhamis da ta gabata da safe kuma dukkan fasinjoijin sun kone yadda ba a a iya gane fuskokinsu ba, bayan da motar ta kama da wuta a nan take.
An ce motar ta pail loader, ta kwace ne daga kan hanaya, inda ta auka wa motar ta Bas da ke kan hanya.
Kakakin rundunar ‘ yan sandan jihar Nnamdi Omoni, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce, mutum daya ne kawai ya rayu daga cikin fasinjojojin amma Shi ma ya samu mummunan kuna a yanzu haka yana asibiti ana yi masa magani.