Sabo Ahmad" />

Jami’ar Sojoji Ta Dauki Dalibai 1,016 A Bana

Sabuwar jami’ar sojoji da aka bude a garin, Biu, da ke jihar Borno ta dauki dalibai 1,016 a shekarar karatu ta 2018 zuwa 2919.
Da yake jawabi wajen bikin yi wa daliban maraba wanda kuma shi ne na farko a tarihin jami’ar a shekaranjiya Alhamis, shugaban jami’ar Farfesa Dabid Malgwi, ya ce, an dauki daliban ne bisa ka’idar da Hukumar JAMB ta kafa.
Mista Malgwi ya yi bayanin cewa, an dauki dalibai 202 a Tsangayar “Computing” sai dalibai 180, a Tsangayar “Engineering”, sai 104 a Tsangayar “Enbironmental Sciences”, sai 369, Tsangayar “Management and Social Science”, sannan sai dalibai 161 na Tsangayar “Natural and Applied Sciences”. Haka kuma jami’ar ta dauki dalibai 1,000 wadanda za su maimaita karatunsu na sakandire.
Saboda haka, sai ya gargadi daliban da su nisanta kansu daga aikata dukkan wasu laifuka, kamar shiga kungiyar asiri da satar jarrabawa da kuma shigar banza.
Mista Malgwi ya tabbatar da cewa jami’ar na da cikakken tsarin kare rayuka da dukiyoyin dalibanta har ma da makawabtanta, saboda haka sai ya bukaci daliban da zarar sun ga wani abu da ba su fahimta ba su gaggauta sanarwa domin a dauki matakin da ya dace.
Shi ma a lokacin da yake rantsar da daliban, Rajistaran jami’ar Birgedita Janar S. Ibrahim, ya kara jaddada cewa dukkan daliban da aka dauka, an dauke su ne bisa cancanta.
Shi ma a nasa jawabin shugaban rundunar sojojin ta Nijeriya kuma shugaban majalisar gudanarwar jami’ar Laftanar Janar Tukur Brutai, yaba wa ministan ilimi ya yi, Malam Adamu Adamu, bisa kokarin day a yin a tabbatar da wannan jami’a.
Wanda mai bayar da shawara a kan harkokin shari’a Chukwuemeka Okwankwo,na jami’ar ya wakilce shi, Buratai ya ci gaba da yabawa kwamitin da suka tabbatar da wannan jami’a bisa jajircewar da suka yi na ganin wannan makaranta ta tabbata.
A karshe ya bukaci daliban su kasance masu kiyaye dokokin wannan jami’a yadda bayan sun gama za su zama wakilai nagari cikin al’umma.

Exit mobile version