Jami’ar Usman Dan Fodiyo Za Ta Samar Da Kundin Tarihin Jihar Zamfara

Jami’ar Usman Dan Fodiyo ta sha alwashin samar da kundin tarihin lardin Jihar Zamfara, wanda ya kunshi tarihin da, da kuma arzikin da ke ciki da kuma matsalolin da ke addabar Jihar don magance su.

Daraktan yada labarai da wayar da kan al’umma na gidan gwamnatin jihar Zamfara, Malam Yusuf Idiris ne ya bayyana haka a takardar da ya rabawa manema labarai a Gusau Babban birnin jihar Zamfara .

Malam Yusuf Idiris ya bayyana cewa jami’ar ta bayyana hakan ne a taron kasa da sahsen kimiyya da addanin musulunci ya shirya na kwanaki hudu a jami’ar dake Sokoto. Kuma taron samar da kundin tarihin jihar, zai kunshi duk bayanai akan jihar bakidaya na Ma’adanan da Allah ya yi mata da kuma abubuwan tarihin da take da su da kuma yadda jihar za ta ci gaba ta kowane bangare.

” Don ganin shirin bai samu Matsala ba, gwamna Bello Matawallen Maradun ya ba Kwamitin gudunmuwar Naira miyan bakwai da rabi 7.5, ta hannun sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bala Bello Maru .

Kuma wannan taron an yi shi ne karkashin jagorancin, tsohon gwamnan jihar Sokoto Malam Yahaya Abdulkarim, wanda ya wakilci, mai maitaba sarkin Musulmi Sa’adu Abubakar na III, da Sarakunan Jihar Zamfara, karkashin jagorancin shugaban majalisar Sarakunan, Alhaji Attahiru Ahmad, Sarkin Zamfaran Anka .

Exit mobile version