Connect with us

LABARAI

Jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto Ta Yi Rashin Jigo

Published

on

A yau ne Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo dake Sokoto (UDUS) suka tashi da alhinin rasuwar Farfesa Lawalli Abubakar, wanda yake shi ne mataimakin shugaban Jami’ar wato DVC (Academic).

Farfesa Lawali ya rasu ne da safiyar yau Talata, 28 ga watan Afrilu a garin Sokoto bayan gajeruwar rashin lafiya. Za a bizne shi ne bayan sallar Azahar bayan dangi, ‘ya’ya, iyalai da abokai sun hadu sun yi bankwana da shi.

Marigayi Farfesa Lawali kafin nadin da aka yi masa a matsayin DVC, Academic, ya rike mukamai da daman gaske a matakin gudanar da Jami’ar.

Sannan memba ne a kungiyar Malaman Jami’o’i, wato ASUU inda harma ya taba rike mukamin shugaban ASUU na Jami’ar, sannan ya kasance cikin kwamitoci daban-daban a matsayin jiha da kasa.

 
Advertisement

labarai