Sabon shugaban jami’ar Maitama Sule, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, ya bayyana kudurinsa na bai wa ‘yan asalin Jihar Kano fifiko wajen daukar dalibai, domin samun gurbin karatu mai inganci.
Shugaban, ya bayyana hakan ne, a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a fadarsa da ke Kofar Kudu, cikin birnin Kano.
Shugaban, ya nemi masarautar Kano da ta taimaka wajen yin kira ga Gwamnati don samun kammala wasu ayyuka, kamar dakunan kwanan dalibai, da sauransu.
A nasa jawabin, Mai martaba San-Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana kudurin masarautar kan taimaka wa hanyar da za ta inganta ilimi, sannan ya yi kira ga Gwamnati da ta taimaka wajen kammala ayyukan da jami’ar ke bukata.