A yayin taron manema labaru karo na 2 da aka shirya a nan Beijing, dangane da batun jihar Xinjiang ta kasar Sin a kwanan baya, wani jami’in jihar ya musunta karyar da masu adawa da kasar Sin da ke ketare suka yi, cewa wai ana sa ido kan mutane a jihar ta Xinjiang, tare da tilasta wa mutane yin aiki, har ma wai an yi kisan kare dangi a jihar.
A yayin taron, mataimakin darektar sashen kula da yayata jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin na kwamitin jihar na JKS Xu Guixiang, ya musunta karyar bisa hakikanin abubuwa da alkaluma, tare da yin karin bayani kan abubuwan da kasar Amurka ta yi, wajen keta hakkin dan Adam bisa tarihi, da ma halin da take ciki a yanzu.
Xu ya ruwaito alkaluman kididdiga dake cewa, yawan ‘yan kabilar Uyghur a Xinjiang ta karu daga mutum 10,171,500 a shekarar 2010 zuwa 12,718,400 a shekarar 2018, adadin da ya karu da kaso 25.04, yayin da yawan ‘yan kabilar Han ya karu daga 8,829,900 zuwa 9,006,800, adadin da ya karu da kaso 2 bisa dari. Ya ce azahiri take cewa, karuwar yawan ‘yan kabilar Uyghur ya fi karuwar al’ummar jihar baki daya, da karuwar ‘yan kananan kabilu, da ma karuwar ‘yan kabilar Han.
Haka zalika kuma, Xu ya nuna cewa, a daya hannu ana cin zalin al’ummu marasa rinjaye a kasar ta Amurka, wadanda aka dade ana nuna musu bambanci bisa tsari a fannonin siyasa, tattalin arziki, al’adu, da sauran sassan zaman al’ummar kasa.
Ya ce mutuwar George Floyd, wani Ba’amurke dan asalin Afirka a bara, da zanga-zangar da ta biyo bayan mutuwarsa, sun sake nuna yadda aka dade ana fama da wariyar launin fata bisa tsari a Amurka, lamarin da ya sanya al’ummu marasa rinjaye su kasa yin numfashi. (Tasallah Yuan)
Allurar Rigakafin Da Sin Ta Samar Na Da Inganci
Ran 30 ga watan Disamba na shekarar bara, bayan allurar...