Connect with us

LABARAI

Jami’iyyar APC Ta Firgita Da Karbuwar Da Kwankwaso Yake Yi — CUPP

Published

on

A cikin kimanin awowi ashirin da hudu da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da tsayawar takarar shugaban kasar nan a karkashin inuwar jamiyyar sat a PDP, ya sanar da cewar hanshi da gwamnatin tarayayya ta yin a yin amfani da filin Eagle Skuare duk da cewar ya biya kudinsa na yin amfani da filin, hakan ya nuna Shugaba Muhammadu Buhari ya razana ne da karbuwar da Kwankwaso yake kara samu a kasar nan daga magoya bayansa. Sai dai, a martanin gaggawa da Ministan Birnin Tarayya Mallam Muhammad Bello ya mayar ya tambayi tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daya gabatar da hujjar  cewa, an amince masa yin amfani da filin. Ministan ya mayar da martanin ne ta hanyar mai taimaka masa na musamman Abubakar Sani a hirarsa da jaridar Banguard, ya ce,  Kwankwaso ya rubutar takardar neman izinin yin amfani da filin ? Ya fito ya nuna mana  wasikar  da aka amince masa yin amfani da filin. Amma a sanarwar da ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na Kwankwaso  suka raba wa manema labarai ranar Talata a Abuja, sun bayyana bakin cikinsu a kan kin amince masu yin amfani da filin bayan an basu tabbacin yin amfani da filin, inda gwamnatin ta buge da wasu dalilai mara tushe balle makama. Sanarwar ta ci gaba da cewa,“A wasikar da muka bayar ta neman izinin yin amfani da filin mai kwanan wata 27 ga watan Agustan shekarar, Usman Mukhtar Raji, mai kula da filin ne ya sanya mata hannu aka kuma snya mana ranar 28 ga watan Agusta na shekarar 2018 don Kwankwaso ya kaddamar da kansa a takarar ta shugaban kasa.” A cewar sanarwar, “Ofishin na yakin neman zaben na Kwankwaso hana yin amfani da filin zagon kasa ne da gwamnatin tarayya ta yi don danne ‘yan adawa da kuma yi wa dimokiradiyya zagon kasa, amma abin takaici filin wanda kamfanin Integrated Facility Management Serbices ke kula dashi a ranar talatar data wuce sai suka hana mana yin amfani da filin,inda suka umarce mu damu basu takardar izinin yin kaaddamawar da muka karbo daga gun yansanda bayan cewar an amince mana muyi amfani da filin. Sanarwar ta ci gaba da cewar, “hana mu yin amfani da filin ba zai kashe mana kwarin gwaiwa ba kuma zamu ci gaba da kaddamawarwar ta Kwakwaso domin babu wanda ya iya ya danne mana yancin mu na zirga-zirga.” A wata sabuwa kuwa, gamayyar jamiyyu ta CUPP, sun yi tir da hana Kwakwaso kaddamar da kansa a matsayin dan takarar shugaban kasa a filin duk da cin kashin da ake yiwa yan adawa a cikin shekaru uku da suka shige. Kakakin gamayar na jamiyyun Ikenga Ugochinyere  ne ya sanar da hakan a ganwarsa da manema labarai a a Abuja a ranar talatar data wuce, inda yaja kunnen APC kan kada ta jefa kasar nan a cikin wata matsala da za ta janyo daukar doka a hannun jama’a. Acewarsa, “ wannan bashi nekaro na farko bad a aka taba yin hakan  ba domin sun taba dakatar da hana karbar  Kwankwaso a jihar  Kano suna son su dakatar dashi nekawai saboda shugaban kasa ya firgita da tsayawar  Kwankwaso takarar shugaban kasa a 2019.Ya kara da cewar, wannnan zagon kasa ne daga da kuma nuna mulkin daniyya a Nijeriya kuma bai kamata yan Nijeriya su sake yin kuskuren zabar Buhari ba a 2019. Ya bayyaana cewar,  Kwankwaso yana son ya kaddamar da kansa neman shugabancin kasar nan a iniuwar PDP wadda tana daya daga cikin jamiyyar da suka yi gamayya da  CUPP kuma muna son mu sanar day an Nijeriya cewar, wannnan danniyar da ake son za a a yi ba zamu yarda da ita ba domin akwai hadari a cikinta musamman yadda yansanda suka hana yin amfani da filin don wani yana son ya tsaya takarar shugaban kasa.

Dandalin na  Eagle Skuare, an gina shi nedon yin taro irin wannnan in kuma mutane suna son yin amafanoi da shi suna biya kuma  Kwankwaso ya shiya don karbar takadar neman tsaywa takararsa da kuma fam dinsa na tsawa a wannan satin bayan ya kaddamar da kansa.

A karshe ya ce, ‘yan takara biyu a PDP, Gwamna Ibrahim  Dankwambo  na jihar Gombe da kuma Sule Lamido sun sa yi nasu fam din na tsaya wa takarar  shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: