Daga Abubakar Abba
Akwai bukatar Jami’oin dake a nahiyar Afrika su jagoranci yin amfani da fasahar zamani da kere-kere don a bunkasa fannin noma a kasashen dake cikin nahiyar.
Kwararru a fannin aikin noma ne suka yi nuni da hakan a taron shekara-shekara na jami’oin dake a yankin na Afrika da ya gudana a Jami’ar Cape Coast dake kasar Ghana.
Ganin cewar kasashen suna da sama da kashi 60 na alumomin su da suke yin noma, fannin na noma ana sa ran zai kuma kara samar da dimbin ayyukan yi, musamman ga matasa.
Sai dai, idan jami’oin kasar nan basu bai wa bincike mahimmanci ba da kuma samar da dabaru za’aci gaba da barin fannin aikin noma a baya a Nijeriya duk da cewar Nijriya Allah ya wadace tad a kasar yin noma mai kyau, inda har za’a iya fitar da amfanin gonar dake ake nomawa a kasar zua kasuwanni duniya.
Mataimakin Darakta kuma wakilin yanki a nahiyar Afrika a sashen abinci da amfanin goma na hukumar FAK Dakta Abebe Haile-Gabriel ya sanar da cewa, nasarar nahiyar Afirka na muradun karni na (SDGs) ya danganta ne kan irin yadda aka mayar da hankali wajen magance kaulubalen da ake fuskanata.
A cewar Mataimakin Darakta kuma wakilin yanki a nahiyar Afrika a sashen abinci da amfanin goma na hukumar FAK Dakta Abebe Haile-Gabriel, kasashen dake a nahiyar Afrika har yanzu an barsu a baya wajen yin amfani da fasaha don bunkasa fannin noma a kasashen nasu.
Dakta Abebe Haile-Gabriel ya ci gaba da cewa, dumamar yanayi yana daya daga cikin kalubalen da manoma suke fuskanta a lokacin da suka yi girbin amfanin gonanak su, inda ya yi nuni da cewa, wannna matsala ce da jami’oin zasu iya shawo kanta amma idan jami’oin sun mayar da hankali wajen gudanar da yin bincike da kuma mayar da hanakli wajen yin amfani da fasaha a fannin noma.
Har ila yau, masanan sun sanar da cewa, shigo da dabarun noma na zamani zuwa kasar nan, zai taimaka wajen bunkasa samar da abici da kuma kawar da yunwa, musamman a karkara.
Ya jadda da cewa, ya zama wajibi jami’oin mu su mayar da hankali wajen gudanar da bincike don a kara bunkasa fannin noma a Nijeriya.
Ya ce, hukumar ta FAO da kuma RUFORUM suna shiryin fara horasa da daliban da aka yayae daga jami’oin koyon aikin noma, inda zasu shafe watanni shida a horasawar yadda zasu bazama gudanar da yin bincike a fannin.
Babban Sakataren na RUFORUM Farfesa Adipala Ekwamu ya yi nuni da cewa, jami’o zasu taimaka matuka wajen gudanar da bincike a fannin na noma.
A cewar Babban Sakataren na RUFORUM Farfesa Adipala Ekwamu RUFORUM ya na akan gaba wajen samar da tsare-trsaren bunkasa fannin noma ta hanyar aikin noma ta fasahar zamani a nahiyar Afirka.