Connect with us

LABARAI

Jam’iyar NRM Ta Yi Sabbin Shugabanni A Zamfara

Published

on

Jam’iyar, NRM,reshen jihar Zamfara, ta yi sabbin shugabani na riko, dan gudanar da zabe nan da mako biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya Umar ta. Shugaban Jam’iyyar na Kasa Sanata Saidu Dansadau ne ya bayyana haka a lokacin gangamin jam’iyyar a Gusau Baban birnin jihar Zamfara.
Sanata Muhammad Saidu Dansadau ya bayyana cewa ‘Jam’iyyar, NRM, jam’iyya ce, mai cetun aluma kuma mai bin kaida da ba kuwane dan kasa hakinsa da dan jam’iyya.
Dan haka masu reke da nukaman jam’iyya tun bayan yimata Rijista, kundin tsarin mulkin jam’iyya ya muna cewa wa’adin su ya cika dan huka muna godiya da gagarumar gudunmuwar da su ka bada. Kuma yanzu haka kofa abude take ga duk mai san tsayawa takara na mukamin jam’iyya tun daga matakin jiha da na kananan hukummomi da na tarayya.
Sanata ya kuma bayyana cewa, kofa abude take ga duk mai san shigo wa wannan jam’iyya da ya je ofishinta dan amsar katin shigar kuma duk dan jam’iyya na da ikon shiga takara na kuwane mukami, don bada gudunmuwar ciyar da jam’iyyar gaba
A takardar banyan taro da aka raba wa manema labarai ta bayyana sabbin shugabanin na riko su ne kamar haka, Alhaji Abdullahi Muhammad Lakwaja Anka, a matsayin shugaban jam’iyyar,na jiha sai kuma Alhaji Muhammad Janjuna.
Anka a matsayin Sakataren jiha sai kuma manbobin su wadanda su ka hada da Hon Bala Muhammad Dansadau da Alhaji Isah Ahmad Moriki da Hajiya Aisha Ibrahim Gusau da Alhaji Tijani Jibril da Alhaji Mustafa Enginiya da Malam Bilyamunu Shuaibu Dansadau da Alhaji Umar Ayo da Alhaji Bashir Magami da kuma Alhaji Rabiu Mohammed Kaura.
Shugaban na riko Alhaji Abdullahi Lakwaja Anka ya bayyana godiya sa ga Allah da ya sa aka ga cancantar su aka zabo su Shugabancin jam’iyyar na riko, har zuwa lokacin gudanar da zabe.
Alhaji Lakwaja Anka ya tabbtar da cewa, majalisar za ta yi iyaka kokarinta na ganin ta ba kowane dan jam’iyya hakinsa, kuma zamu tafi da ‘yan jam’iya kafada da kafada don samun nasarar jam’iyya a jiha da kasa baki daya.
Kuma muna jinji a ga gwarzo kuma jigo ga Jam’iya, Sanata Muhammad Saidu Dansadau, a kan kokarinsa na ganin wannan jam’iyya ta shiga lunguna da sakona na kasar nan, da fatan Allah ya cika masa burinsa na ganin jam’iyyar NRM ta lashe duk zabubkan da za a gudanar a shekara ta dubu biyu da sha takwas, tun daga matakin Dan majalisar jihar da na tarayya da ‘yan majalisar datawa da gwamnoni da shugaban kasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: