Umar Faruk" />

Jam’iyyar Adawa Ta PDP Ta Yi Babban Kamu A Kebbi

Jam'iyyar Adawa

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kebbi tayi babban kamu a Birnin-Kebbi, inda wani babban jigo a jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta Kebbi, Alhaji Abdulmalik Haliru wanda aka fi sa ni da (Milton) tare da magoya bayansa sun chanza sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP a jiya a Birnin-Kebbi.

An gudanar da taron bikin karbar babban jigo dan siyasar ne tare da magoya bayansa a babban ofishin Sakatariyar PDP da ke a Birnin-Kebbi a jiya. Wanda shugaban mazabar Nasawa 1, Alhaji Ibrahim Abdullahi tare da shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Mulki ta Birnin-Kebbi, Alhaji Abubakar Kane da sauran mukaraban Jam’iyyar suka karbi Alhaji Abdulmalik Haliru (Milton) da kuma magoya bayansa a ofishin Jam’iyyar adawa ta PDP da ke a Birnin-Kebbi.

Hakazalika, a nan take shuwagabannin mazabarsa ta Nasarawa 1, suka bashi katin shedar zama dan Jam’iyyar PDP tun daga mazabarsa har zuwa matakin kananan hukumomi har zuwa jihar, domin tabbatar da cewa ya zama ciken dan Jam’iyyar PDP a jihar Kebbi da matakin kasa baki daya.

Haka kuma kafin karbarsa a ofishin Jam’iyyar PDP sai da ya bada shedar takarda da ya rubuta wa Jam’iyyar APC na sanar da ita cewa ya fice daga Jam’iyyar APC ya kama koma Jam’iyyar adawa ta PDP, sannan aka karbe Shi a Jam’iyyar ta PDP a daga mazabarsa .

Da suke jawabi yayin karbar babban dan siyasa a jihar ta kebbi kuma dan kasuwa, Alhaji Abdulmalik Haliru Milton, shugaban mazabar Nasarawa 1, da shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Mulki ta Birnin-Kebbi, Alhaji Ibrahim Abdullahi, Alhaji Abubakar Kane sun bayyana jinda dinsu da murna kan dawo war Abdulmalik Haliru Milton tare da magoya bayansa Jam’iyyar PDP domin dawowarsa gida ne yadawo.

Saboda haka sun yi Kira ga Abdulmalik Haliru Milton da magoya bayansa suyi amfani da damar dawowarsu na kara jayo wasu mutane su dawo Jam’iyyar PDP kamar yadda suka dawo. Sun kara da cewa kofar Jam’iyyar PDP a bude ta ke ga duk wanda ke son dawowa ko shiganta a matsayin sabuwar jam’iyyarsa dukan su ana maraba dasu ba tare da nuna wani banbanci ba ko kabilanci na yare ko addini ba .

Bugu da kari suna godiya ga magoya bayan Jam’iyyar PDP a matakin mazabu har zuwa matakin jihar kan irin hakuri da kuma jajircewa da suke yi duk da cewa ba Jam’iyyar PDP ke mulki ba.

Bisa ga hakan su ci gaba da tallata Jam’iyyar ga jama’ar jihar ta Kebbi da kuma kara kokarin jawo mutane su dawo cikin Jam’iyyar domin nan da shekara ta dubu 2023 Jam’iyyar PDP ta koma mulki a jihar Kebbi da sauran jahohin kasar nan kai har ma shugabancin kasar Nijeriya baki daya.

Exit mobile version