Connect with us

LABARAI

Jam’iyyar APC A Bauchi Ta Kalubalanci Shugaban Majalisar Wakilai

Published

on

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Bauchi ta bayyana cewar Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara sam ba dan goyo da zani ba ne, domin ta yi masa sha tara na arziki, kana ta rufa masa asiri wanda har ya kai matsayin da yake a yau, amma kuma ita ce zai kunce wa zani a kasuwa.

Jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi ta shaida hakan ne a jiya a Bauchi a sa’ilin da suke maida wa Dogara martani kan kalaman da ya furta a lokacin da ya koma cikin jam’iyyar PDP, inda shi Dogaran ke shaida cewar jam’iyyar APC a matakin jihar Bauchi da kasa ba ta iya cimma alkawuran da ta dauka wa jama’a ba.

Dogara ke cewa, “Ina daga cikin jama’an da suka gina jam’iyyar APC a jihar Bauchi, da ni aka zaga yakin neman zabe, amma kuma sam ba zan iya fada muku alkawari guda daya tak da jam’iyyar ta iya cikawa ba. A matakin kasa ma ga halin da ake ciki ai.

“Don haka na yanke shawarar shiga cikin ‘yan uwana maza da mata a cikin wannan jam’iyya mai dumbin albarka ta PDP domin ci gaba da gina jihar Bauchi da kasa baki daya,” Kamar yadda wani bangare na jawabin Dogaran ke cewa.

To sai dai, a kakkausar martanin jam’iyyar APC na jihar Bauchi, ta shaida cewar sam ita ba ta gaza ba, sai dai shi Dogara din ne ya gaza, tana mai shaida cewar ita ta yi nasarar kyautata rayuwar jama’a a jihar da kasa baki daya don haka zancen Dogara soki-burutsu ne kawai ya shaharara domin boye aibinsa.

Da yake karanta wasikar da jam’iyyar ta fitar wa manema labaru, babban mai baiwa jam’iyyar APC a jihar Bauchi shawara kan harkokin shari’a, Barista Rabi’u Garba ya bayyana cewar tun usuli ma Dogara bai mutunta jam’iyyarsu.

A cewar APC, “Zargin da Dogara ya yi na cewar APC ta gaza a jihar Bauchi da kasa wannan zargin ba daidai ba ne. a zahirin gaskiya Dogara ya koma PDP ne kawai don ya tabbatar ba zai kai ga cimma burinsa a karkashin jam’iyyar APC ba.

“Shi ‘Dogara’ ba yanzu ne ya fara irin wannan abun da ya yi a yanzu ba. lokacin da ya shigo jam’iyyar APC ya fahimci jam’iyyar PDP ba za ta tsaida shi a kujerarsa na dan majalisa ba ne sai ya furta irin wannan maganar akan PDP, wannan dalilin ya sanya ya zo APC, inda mu kuma muka amshesa muka wankesa muka yi masa fes aka bashi dama wanda yanzu da wannan damar yake kan kujerar da yake a yau.

“Jam’iyyar APC ta yi wa Yakubu Dogara gata sosai wanda bai kamata ya butulce wa jam’iyyar ba, An ce yaba kyauta tukuici, muna da tarihin ya aikata haka a baya, don haka mu muna ganin ya koma PDP ne kawai a bisa dalilinsa na radin kansa ba wai don APC ta gaza ba,” Inji takardar da APC reshen jihar Bauchi ta fitar na martani.

APC ta ci gaba da cewa, “Muna tabbatar wa jama’a cewar mu ba mu gaza ba, shi ne ya gaza. APC ta yi aiyukan raya kasa a Nijeriya masu tulin yawa, an samar da tsaro, an habaka tattalin arziki, APC ta toshe kafar sata, an habaka sashin noma, an dakile cin hanci da rashawa, an habaka kananan ‘yan kasuwa. A jihar Bauchi an yi aiyuka masu tulin yawa jam’iyyar APC ta bunkasa ilimi, an rage talauci an taimaki mata da mata  an samar da ruwa a jigar da sauran dumbin aiyukan da APC ta yi, don haka zancen Dogara soki-burutsu ne kawai,” Inji Garba

Jam’iyyar ta shaida cewar dalilin fitar Dogara daga jam’iyyar shine ya tabbatar ba za su tsaida shi ba, “ya tabbatar muddin ya zauna a jam’iyyar APC, domin muna da tarihin cewar tun da APC ta bashi dama ya tafi a 2015 bai taba zuwa sakatariyar jam’iyyar APC na jihar Bauchi ba, bai ma bayar wa jam’iyyar muhimmanci koda zama aka gayyaceshi ba ya zuwa. Kai bai ma san su waye ne shugabanin jam’iyyar APC a jihar Bauchi ba, dukkanin abun da ake yi a jihar Bauchi babu ruwansa.

“Ko da a zaben cike gurbin Sanatan Bauchi ta Kudu da aka yi kwanan nan, jam’iyyar APC ta fadi a mazabar Dogara ‘Bogoro kenan’ wannan ke tabbatar wa duniya cewar shi Dogara bai taimaka wa jam’iyyar ta kowace fuska. Sannan zaben da aka yi na APC Dogara bai zo ba bai kuma halarci dukkanin zabukan da aka yi ba. don haka ne ya san cewar tun da bai taka rawa wajen zaben jagororin jam’iyyar APC ba ya san sune masu zabe ‘delegates’ ba kuma za su tsaida shi ba. wannan kawai shine dalilinsa na ficewa daga cikin jam’iyyarmu, kuma hakan din bai tada mana hankali ba,” Kamar yadda jam’iyyar ta shaida

Da yake karin haske wa ‘yan jarida kan wannan marhalar, shugaban jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmad Nana ya shaida cewar suna addu’ar dukkanin wani butulun da zai bata musu jam’iyya gwara ya yi tafiyarsa ya barsu.

“Ita APC bata iya cin mutuncin ‘ya’yanta ba, kuma bata korar mutum amma duk mutum, duk dan APC da manufarsa ba mai kyau bane, wanda zamansa a cikinmu zai kawo mana matsala muna addu’ar Allah ya taimakemu shi da kansa ya tattara nasa-ya-nasa ya yi gaba.

“A duk lokacin da wani ya fita daga jam’iyyar muna ganin addu’armu ce ta karbu, a duk lokacin da mutum daya ya fita dari suna shigowa,” Inji Uba Nana

“Shi Dogara shine ya gaza ba jam’iyyar APC ba, don haka muna maida masa martani kan cewar mu jam’iyyarmu ba ta gaza ba. masha Allah tun da har mun kai a dale bayanmu a kai matsayin da ake a yau,” Kamar yadda Uba Nana ya shaida.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: