Jam’iyyar APC A Jihar Kebbi Ta Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Kananan Hukumomi

Daga Umar Faruk Birnin Kebbi,

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi ta kaddamar da yakin neman zaben shuwagabannin kananan hukumomin tare da Kansilolinsu a duk fadin kananan hukumomi 21 a jihar da ke tafe.

Idan dai ba a manta ba hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kebbi ta tsayar da ranar 5 ga watan Fabrairun 2022 a matsayin ranar gudanar da zaben shuwagabannin kananan hukumomi da kansiloli a fadin jihar.

Da yake mika tutocin ga ‘yan takarar da jam’iyyar APC a jihar ta tsayar don karawa da sauran jam’iyyu , Gwamna Abubakar Atiku-Bagudu ya bukace su da su koma su sasanta da ‘yan jam’iyyar da suka samu matsala tare da su da kuma wadanda aka sabawa , inda ya kara da cewa ‘yan takarar ba su ne suka fi kowa ba.

Ya ce dalilin zuwan Kamba shi ne da farko a jajanta wa al’umma game da barkewar gobarar kasuwa a kwanakin nan, da kuma kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomi da kaddamar da sabon ofishin jam’iyyar na shiyyar Arewa a garin na Kamba.

A yayin da yake mika godiyarsa ga al’ummar yankin kan zaben jam’iyyar APC a dukkan matakai na zabe, Gwamna Atiku-Bagudu ya kuma nemi kuri’unsu a zaben kananan hukumomin da ke tafe.

Gwamnan ya ce an gina jam’iyyar APC a Kebbi kuma an kafa ta ne bisa adalci inda ya tuna cewa babban Lauyan gwamnatin tarayya na yanzu, Abubakar Malami shi ne dan takarar gwamna na farko da ya bar masa kujerar gwamna a shekarar 2015 sai kuma wasu masu neman tsayawa takara.

“Malam bai shiga jam’iyyar APC ba don zama babban lauya gwamnatin tarayya ba, haka Sanata Muhammad Adamu Aliero dan jam’iyya ne kuma dan uwana ne, ya shiga APC ne ba don ya zama sanata ba, duk wannan nufin Allah ne, inji shi”.

“Saboda haka duk wanda yake ganin yana da wayo ya zama wani abu, kuskure ne babba, fada da juna bai dace da mu ba, sai dai mu rungumi junanmu domin ci gaban jihar.

“Na rantse da Alkur’ani mai girma cewa zan kare gwamnati da kundin tsarin mulkin tarayyar kasar Nijeriya, za ku iya yakar Atiku Bagudu amma ba za ku iya yakar gwamnati ba,” in ji shi.

Haka zakila , Gwamnan ya bukaci kowa da kowa da su kasance masu hakuri da juna idan har za su ciyar da jihar gaba.

Sanata Atiku-Bagudu ya bayyana gamsuwa da cewa mukamin babban Lauyan da Malami ke rike da shi ya share fage ga abubuwa da dama da ba su kirguwa da suka zo Jihar Kebbi.

Da yake jawabi tun da farko, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abubakar Mohammed-Kana ya bayyana cewa saboda kyakkyawan shugabancin Gwamna Abubakar Atiku da na jam’iyyar APC na jiha ne ya samar da ‘yan takarar shuwagabannin kananan hukumomi tare da Kansilolinsu a dukkan fadin Jihar , amma masu ruwa da tsaki a kowace karamar hukuma sun yi taro sun yi muhawara tare da cimma matsaya kan ‘yan takararsu ba tare da wata matsala ba,inji Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi Abubakar Muhammad Kana”.

Ya yaba wa shugabannin jam’iyyar APC na duk kananan hukumomi 21 da kuma godiyarsa mutanen mazabun shiyar Arewa bisa gudunmawar Naira miliyan 50 domin tallafa wa jam’iyyar a zaben kananan hukumomi mai zuwa.

Daga karshe Shugaban ya kara da cewa jam’iyyar APC guda kaya ce a jihar Kebbi, inda ya tabbatar da cewa babu wani bangare a jam’iyyar.

Exit mobile version