Muhammad Shafi’u Saleh" />

Jam’iyyar APC Da Karin Wa’adin Shugabanninta A Adamawa

Tun bayan da jam’iyyun adawa suka hadu suka yi maja, wato suka dunkule waje guda suka kafa jam’iyyar APC, domin tirkarar jam’iyyar PDP mai mulki a babban zaben 2015, lallai kuwa hakar jam’iyyun ya kaisu gaci, inda da gagarumin rinjaye su ka yiwa jam’iyyar da ke rike da madafun iko a lokacin PDP fata-fata.

Madugun canji na jam’iyyar APC a wancan lokacin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya sanar a duk inda ya je kamfe cewa talakawa suyi SAK, wato su zabe duk wanda jam’iyyar hadakar  (APC) ta tsayar a kowani matsayi daga sama har kasa haka kuma talakawa suka yi, domin kuwa kashe tamanin bisa dari na mutanen da jam’iyyar ta tsayar takara sun lashe kujerun a kasa baki daya.

A jihar Adamawa kuwa idan nace jam’iyyar hadakar ta lashe kashi casa’in na zabukan da ya gudana a shekarar 2015, baiyi kuskure ba, domin an kai matsayin da APC ta lashe zaben gwamna ta lashe zaben sanatoci uku na jihar, ta lashe zaben mambobin majalisar wakilai bakwai daga cikin takwas da’ake dashi, haka kuma ta lashe zaben mambobin majalisar dokokin jihar 23 daga cikin 25 na jihar.

Wannan nasara da goyon bayan jama’a, da jam’iyyar  APC ta samu ya tabbatar da karfinta ya maishe da jam’iyyar  jam’iyyar jama’a, ta talakawa, wacce talaka ke jin cewa shi ke da jam’iyyar, wato shi ya kafa ta, domin shi ya fito ya sha zafin rana, ruwan sama na dukansa domin ganin dai mafarkinsa ta neman canji ta kaiga hakkaka.

To sai ba a yi nisa da gudanar da zabukan ba, jam’iyyar ta samu kanta cikin gargada da koma baya lokacin da wacce ke jagorantar jam’iyyar a jihar, ta samu lashe kujerar ‘yar majalisar dattawa mai wakiltar arewacin jihar, wato Satana Binta Masi Garba, inda mataimakinta a lokacin marigayi Alhaji Sha’aibu Yamusa, ya dare kujerarta a matsayin shugaban riko.

Jam’iyyar ta samu koma baya gaya a lokacin shugabancin Sha’aibu Yamusa, sakamakon rashin jitowa dake tsakaninsa da gwamnan jihar Sanata Umaru Bindow Jibrilla, dama wasu jiga-jigan jam’iyyar, hakan ya yi matukar tasiri wajan maishe da harkokin jam’iyyar baya, kusan komai na jam’iyyar ya tsaya cak, ana cikin haka kuma Allah da ikonsa Sha’aibu Yamusa ya rasuwa, lamarin da ya sake jefa jam’iyyar cikin halin niyasu da rudamin shugabanci a jihar.

Sai da aka kai matsayin da kwamitin zartaswar jam’iyyar APC a jihar, sun sanar da cewa sun koma jam’iyyar PDP, sakamakon girman matsalolin da ya da baibaye jam’iyyar APC a jihar Adamawa.

Hakan yasa shugabannin jam’iyyar a matakin kananan hukumomi suka hadekansu waje gudu suka tafi hedikwatar jam’iyyar dake Abuja, suka nemi uwar jam’iyyar da ta amince su zabe shugaban riko a tsakaninsu, ba tare da wata-wata ba uwar jam’iyyar ta amince da hakan domin ceto jam’iyyar daga rudamin da ya baibayeta a lokacin.

Shugabannin jam’iyyar kananan hukumomin ba tare da bata lokaci ba suka zabe Alhaji Ibrahim Bilal, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Michika kuma shugaban kungiyar shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomin jihar 21 (ALGON), a matsayin shugaban rikon jam’iyyar a matakin jihar, wanda kuma uwar jam’iyyar ta amince.

Wannan dai shine matakin farko na kama hanyar ceto jam’iyyar APC daga rudamin da ta shiga a jihar Adamawa, Ibrahim Bilal, ya samu goyon baya da hadinkan shugabannin jam’iyyar, a lokaci guda kuma, yayi amfani da kwarewar da yake dashi a siyasa wajan bibiyan matsalolin da jam’iyyar ta shiga daya bayan daya yana warwaresu, lamarin da yasa jam’iyyar ta samu zama da gindinta da kuma ci gaba da rike kanbunta a Adamawa.

Shugaban jam’iyyar yayi amfani da kwarewarsa na ganin ya dinke baraka da rudun da jam’iyyar ta shiga, cikin karamin lokaci, sai ga gwamnan jihar Umaru Bindow ya dawo ya rike jam’iyyar hanu biyu, haka kuma sauran da suka fusata sun dawo ana tafiya tare, wannan yasa shugaban jam’iyyar ya ziyarci mambobin jam’iyyar a daukacin kananan hukumomin jihar, domin ji daga garesu, suka kuma nema da’a gudanar musu da zaben shugabannin majalisun kananan hukumomin jihar.

Bilal, ya shiga ya fita, ya tisa gwamnan jihar Umaru Bindow a gaba, lamarin da ya kaiga gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a jihar, zaben da shi ma tamkar sauran da suka gabata, jam’iyyar APC ta lasheshi baki daya, kujerun shugabannin kananan hukumomi 21 da na kansiloli 222, in banda kujerar kansila guda da jam’iyyar SDP ta lashe.

Bayan gudanar da zaben kananan hukumomin ne, hukumar zabe ta kasa (INEC), ta gudanar da zaben cike gurbi na dan majalisar wakilai da ke wakiltar kananan hukumomin Demsa da Numan a majalisar wakilai ta kasa, zaben da ‘yar takarar jam’iyyar Talatu Yohana, ta lashe da gagarumin rinjaye.

Haka dai jam’iyyar ta ci gaba da habaka tana jawo manyan wadanda suka yi adawa da ita a zaben 2015, irin su tsohon shugaban hukumar EFCC kuma dan takarar gwamnan PDP a zaben Malam Nuhu Ribadu da tsohon dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar SDP Mista Markus Gundiri, da ‘yar takarar kujerar sanata ta Adamawa ta tsakiya Aisha Dahiru Binina da mamba da ke wakiltar kananan hukumomin Madagali da Michika a majalisar wakilai Adamu Kamale, Dakta Ahmad Modibbo, Reb. Habila Irtifanus, Honarabul Emmanuel Tsamdu, sauran mambobin jam’iyyu da ke majalisar dokokin jihar da jama’arsu duk sun koma jam’iyyar APC.

Haka kuma gungun jama’ar da suka koma jam’iyyar na baya-bayannan shine da jam’iyyar PDP dongurugum bisa jagorancin tsohon maitaimakawa shugaban kasa Goodluck Jonathan kan harkokin siyasa Ahmad Ali Gulak, ta koma  APC bisa kyakkyawar shugabanci da jagorancin da suka yi amanna ke gudana karkashin jam’iyyar a jihar Adamawa.

Ana cikin haka ne kuma sai batun karin wa’adin shugabancin na shekara guda ga shugabannin jam’iyyar a kasa baki daya ya tasu, inda a wani taron majalisar zartaswar jam’iyyar (NEC) na kasa ta sanar da karin wa’adin shugabancin. shi wannan batu na karin wa’adi, wani alfanu jam’iyyar za ta girba karkashinsa a jihar Adamawa?

Bisa la’akari da nasarorin da jam’iyyar ta cimma abaya, ba shakka wannan wata damace da ke nuni da cewa tamkar damara kawai jam’iyyar ta ja, domin fuskantar babban zaben 2019, saboda matakin da kwamitin zartaswar jam’iyyar ta dauka ya sake daureta tam ba ta ko girgiza a jihar, lamarin da ke nuni da a fili take cewa babban zaben mai zuwa jam’iyyar ka’iya lashe kashi casa’in bisa dari idan ma ba dari bisa dari na zaben a jihar ba.

Wannan batu haka yake, domin kuwa har kawo yanzu da babban zaben 2019 ke kara karatowa, jam’iyyar APC a Adamawa cika ta ke ci gaba yi, ta kowace kusurwa da sassan jihar labarin guda ne, canja sheka jama’a suke, suna komawa cikinta, saboda da haka karin wa’adin shekara gudan tamkar lasisin jam’iyyar ta ci gaba da jan zarenta a Adamawa ne.

Exit mobile version