Daga Abdullahi Tumburkai, Kaduna
Wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Katsina sun barranta daga jam’iyyar, inda suka kafa wata mai suna ‘APC Akida,’ wanda suka ce sun haka ne don kwato jam’iyyar daga faduwa zabe a shekarar 2019.
Sun bayyana wannan ne a wani babban taro da suka yi a dakin taro na gidan Sardauna, wanda aka fi sani da ‘Arewa House da ke Kaduna jiya Asabar.
Shugabanin wannan tafiya ta APC Akida Katsina, sun hada da Sanata M.T. Liman, Sanata Sadik ’Yar’aduwa da kuma Dakta Usman Bugaje, sai kuma Sakataren wannan kungiya, Honorabul Barista Abbas Abdullahi Machika.
Alhaji Sada Ilu, Abubakar Sama’ila Isah Funtuwa, Alhaji Tijjani Zangon Daura, Sanata Abdu ’Yandoma da sauran manya-manyan jiga-jigan jam’iyyar APC ta jihar Katsina.
Taron dai ya bayyana cewa dukkan mahalarta taron su koma gidajensu su yi nazari kafin taro na gaba da za a kira kwanan nan a jihar ta Katsina don ci gaba daga inda aka tsaya. Kimanin mutane dubu biyu ne suka halarci taron.
A tattaunawarsa da wakilinmu bayan tashi daga taron, Sakataren kwamitin, Barista Abbas Machika ya bayyana cewa ba za su ci gaba da zura ido su bar wasu na kashe jam’iyyar da suka sha wahala wajen kafawa ba.
Ya ce, ya zama wajibi su yi duk abin da ya kamata don maido wa da jam’iyyar kimarta da aka santa da shi. Ya ce, yadda abubuwa ke tafiya a jihar Katsina, abin takaici ne. Kuma idan suka ci gaba da zura ido, to lallai za a kai al’ummar jihar a baro.
Ya ce, yanzu haka dab ake da a hallaka jihar gaba daya. Saboda haka nauyi ne ya hau kansu don kwato jihar.
Alhaji Kabir Funtuwa, wanda yana daya gada cikin wadanda suka halarci taron, ya shaida wa wakilinmu cewa ya yi matukar farin ciki da halartar wannan taro. Ya ce duk da cewa an kusa a Makara, amma za su koma gida su ci gaba da fadakar da al’umma halin da ake ciki da kuma abin da ya kamata mutane su yi.
Ya ce gwamnatin jihar ba ta tafiya yadda ya kamata, kuma wasu mutane kalilan ne ke juya akalarta. Don haka ya ce kowa a jihar ya san halin da ake ciki. Za su koma gida su ci gaba da fadakar da mutane kafin taron da za a yi nan gaba a jihar.