Connect with us

RIGAR 'YANCI

Jam’iyyar APC Ta Mutu A Kebbi – Abubakar

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban Hukumar Kwastam, Abubakar Gari Malam (Shettiman Gwandu) ya bayyana cewar jam’iyyar APC ta mutu a Jihar Kebbi don haka za su tabbatar da karbar mulki a hannun Gwamna Abubakar Atiku Bagudu a zaben 2019.

Jigon dan siyasar ya bayyana cewar ya kwashe tsayin shekaru 12 yana son ya zama Gwamnan Jihar Kebbi domin bayar da gudunmuwarsa ga ci-gaba da bunkasar Jihar da al’ummarta.

“Jam’iyyar APC ta riga ta mutu a Jihar Kebbi amma duk da haka kada ita sai an shirya tun da ita ke da Gwamnati amma idan muka bayar da cikakken hadin kai to abu ne mai sauki mu kawar da wannan Gwamnatin marar adalci da alkibla ta hanyar zaben jam’iyyar PDP a babban zabe mai zuwa.”

Ya ce yana son al’ummar Jihar da manbobin jam’iyyar PDP su hada kai bakidaya domin kawar da Gwamnatin APC a zaben 2019 wadda ba ta aiwatarwa al’ummar Jihar abin a- zo- a-gani ba hasalima tuni sun fara kakkabe magoya bayan Gwamna Bagudu.

Fitaccen dan siyasar ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai Hedikwatar Jam’iyyar a Birnin Kebbi a ranar Juma’a domin gabatar da takardar bayyana kudurinsa na neman takarar Gwamnan Jihar a zabe mai zuwa yana cewar zai gudanar da Gwamnatin jama’a ta jama’a domin jama’a ba tare da son rai ba.

Shettiman Gwandu ya bayyana cewar idan Allah ya bashi nasarar zama mutum mafi daraja ta daya a Kebbi zai bunkasa Jihar ta hanyar gudanar da muhimman ayyuka masu alfanu wadanda za su yi tasiri ga al’umma tare da cewar zai inganta aikin gona da yin karin haske da cewar shirin bunkasa aikin gona musamma shirin bada bashi na (Ancho borrowers) karya da yaudarar da ke ciki ta fi gaskiyarsa yawa domin idan har an tallafawa manoma yadda ya kamata to da ci-gaban da za a samu ya fi haka yawa don haka ya ce idan ya yi galaba Gwamnatinsa ta manoma ce.

Ya ce idan ya kai ga nasara zai bayar da kulawar musamman ga sha’anin kiyon lafiya ba kamar yadda Gwamnatin Kebbi ke yi ba na gina asibitoci amma babu ma’aikata da kayan aiki yana cewar zai inganta fannin, samar da kwararrun ma’aikata da magunguna da kayan aiki na zamani.

“Zan taka muhimiyyar rawa wajen bunkasa Jihar mu mai albarka, bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Duk abin da nake yi ina sa Jihar Kebbi a sahun gaba, don haka idan muka samu nasara jama’a za su amfana da canjin da za mu samar. A fannin ayyuka za mu baiwa jama’a damar gabatar da ayyukan da suke so a aiwatar masu, haka ma a wajen rarraba mukaman siyasa kama daga Kwamishina da Mashawartan Gwamna duka jama’a ne za mu baiwa damar kawo wadanda suke so su jagorance su domin ni kashin kaina ba ni da zabi face zabin jama’a.” Ya bayyana.

Dan takarar ya bayyana cewar siyasarsa ba ta kudi ba ce kuma ba siyasar a mutu ko a yi rai ba ce “Siyasa Shettima, ta mutunci da amana ce, don haka ina kira da a hade kwadayi a kuma hada kai domin samun nasara. Idan muka kai ga nasara, ba mutum daya ne ya yi nasara ba, nasarar ta mu ce bakidaya.” Ya jaddada.

Babban jigon dan siyasar ya bayyana cewar yana fatar za a samu maslaha wajen tsayar da dan takarar Gwamna ba tare da gudanar da zaben fitar da gwani ba, amma a cewarsa idan ta kama ba a samu sulhu ba to a shirye yake ya shiga zaben share fage kuma zai nemi goyon bayan wakilai ta hanyar shugabannin jam’iyya wadanda ya ce su ne gaba a kodayaushe.

Shettiman Gwandu bayyana cewar siyasar goyon baya ita ce siyasa ba wai siyasar tilastawa ba don haka ya yi kira ga wakilai masu zaben fitar da gwani da cewar su rika gudanar da zabe bisa ga cancanta da hangen nesa ba tare da karbar na goro domin zaben wani ba yana cewar an jima a na cutar wakilai ta hanyar ba su kudi kalilan wanda daga karshe su rika cewa sun tura mota ta burbude su da hayaki.

Ya ce “Yau shekaru 12 ina neman zama Gwamna kuma sai lokacin da Allah ya kaddara zan samu. Zan zagaya sassan wannan Jihar domin neman goyon bayan jama’a domin bunkasa jihar mu shine babban burina.” In ji shi.

A kan dangantakar da ke akwai tsakaninsa da jigon PDP kuma dan takarar jam’iyyar a zaben 2015, Janar Sarkin Yaki Bello wanda a yanzu haka yake kalubalantar Gwamna Atiku Bagudu a kotu domin warware takaddamar zaben, ya bayyana cewar dangantakar su kyakkyawa ce.

Ya ce “Da ni da Janar Sarkin Yaki abu daya muke, uwa daya uba daya. Ina tare da Janar a wannan shari’ar da yake yi, kuma wallahi na fi son a ce yau ya samu nasarar wannan shari’ar wato kotu ta tabbatar da shi a matsayin Gwamna. Ina tabbatarwa jama’a cewar ko na yi nasarar zama dan takara kuma ko na yi nasarar zama Gwamna idan doka ta aminta ta kuma baiwa Janar kujerarsa to zan sauka in bar masa.” Ya bayyana.

A yayin da yake gabatar da jawabinsa Shugaban Jam’iyyar PDP Alhaji Haruna B. Sa’idu ya bayyana Shettiman Gwandu a matsayin halastacce kuma tsayayyen dan jam’iyya kuma masoyin Kabawa wanda a baya ya so zama Gwamna amma Allah bai nufa ba.

“Al’umma sun zabe shi, sun kuma so ya zama Gwamnan Jihar Kebbi, amma Allah bai nufa ba, bakin haure suka yi galaba, amma Shettima bai karaya ba ya ci-gaba da fadi tashi tare da rike jama’arsa da kuma kyautata masu har zuwa wannan lolacin da ya sake fitowa takara.”

Ya ce “Allah ya tabbatar, mutane sun sani, wadanda ke son gaskiya sun sani, Abubakar Malam mutum ne wanda ke da kyakkyawar mu’amala da mutane, wanda kuma ke son gaskiya da aiki da gaskiya.” In ji shugaban na PDP.

Tun da fari a jawabinsa fitaccen dan siyasa Alhaji Umaru Technical (Wamban Yauri) ya bayyana cewar yadda jama’a suka fito ba masaka tsinke suka tarbi dan takarar tare da halartar taron ya nuna cewar Shettiman Gwandu ya samu gagarumar karbuwa kuma yana fatar jam’iyyar PDP za ta samu gagarumar nasarar lashe zabe tare da kafa Gwamnatin Jihar Kebbi a 2019.
Advertisement

labarai