Jam’iyyar APC Ta Shirya Taro Kan Jin Ra’ayoyi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta shirya wani gagarumin taron jin bahasi kan ra’ayoyin jama’a dangane da sake fasalin Nijeriya, wanda ya kunshi jihohin Bauchi, Gombe da kuma Yobe da nufin jin ra’ayoyi da bahasin jama’a dangane da sabunta fasalin Nijeriya da suka hada kan abubuwa kusan sha biyu. Taron wanda ya gudana a karkashin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Chief John E.K Odigie Oyegun, wanda ya gudana a dakin taro na Multi-Purpose da ke Bauchi ranar Litinin.

Taron ya tabo batutuwa goma sha biyu 12 da ke kunshe cikin tsarin sake fasali ga kasar Nijeriya, da suka hada da kirrirowa ko kuma hade jihohi, tsarin rabon arzikin kasa, raba karfin iko a tsakanin bangaren Majalisar zastaswa da dokoki, da kuma bangaren Shari’a, halascin tsayawa takara ba tare da tsayawa a karkashin kowace jam’iyya ba, cin kashin kan Majalisun Kananan Hukumomi da dai sauransu muhimman batutuwa da aka tattauna a wajen.

Da yake jawabi a wajen taron baje kolin ra’ayoyin sake fasali wa kasar, tsohon Gwamnan jihar Edo, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin jin ra’ayoyin na wannan yankin, Farfesa. Sen. O.A Osunbor ya ce wannan matakin domin baiwa al’umma damar tattauna muhimman batutuwa da suka shafi kasar Nijeriya, mataki ne da ya yi daidai da tsarin jam’iyyar APC. Ya ce, kuma suna samun ra’ayoyi mabambanta, inda ya ce daga baya kwamitin zai tattara abubuwan da ya samu a wajen wannan taron.

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Borno, Abdulkarim Bello, wanda Dakta Waziri Dogo ya wakilta ya tufa albarkacin bakinsa kan taron, inda nuna jin dadinsa game da yadda taron ya gudana.

Shi kuwa mai masaukin baki, Gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar, wanda ya samu wakilcin mukaddashinsa, Alhaji Nuhu Gidado ya bayyana cewar aikin kwamitin a matsayin aiki ne mai matukar muhimmanci da kuma fa’ida. A cewarsa, hakan ka iya baiwa al’umma damar kusantowa kusa da gwamnati da kuma shiga domin a dama da su ta fuskacin bayyana ra’ayoyinsu da kuma manufarsu wajen gabatar da fasalin kasa. Kana hakan zai taimaka wa dangantar siyasa da su al’ummar.

A hirarsa da manema labarai, Mataimakin Gwamnan jihar Kogi, Elder Simon Achuba, wanda kuma mamba ne a cikin kwamitin jin bahasin ya bayyana cewa a yayin taron sun amshi ra’ayoyin jama’a da kuma kungiyoyin jama’a da daman gaske, wanda hakan zai taimaka wajen sahale hakikanin abubuwan da suka kamata jam’iyya mai ci ta sanya a gaba.

Ya ce, “Hakimai, shugabanin jama’a, kungiyoyi masu zaman kansu da sauransu duk kun ga sun zo sun gabatar da jawabansu a wajen taron nan, hakan zai bada dama a samu sakamako mai kyau.”

Elder Simon ya ce a karshe dai za su tattara dukkanin rahotonin da suka samu a kowane yanki domin gabatar wa shugaban jam’iyyar na kasa don neman mataki na gaba domin ci gaba da inganta wannan kasar ta Nijeriya.

LEADERSHIP A YAU ta rawaito cewa kungiyoyin fararen hula da kungiyoyi masu zaman kansu da dama ne suka gabatar makalolinsu, bukatunsu da kuma korafe-korafensu a yayin wannan taron. Kungiyoyin sun hada da ‘yan kasuwa, kungiyar mata, kungiyar matasa da kuma bangarorin al’umma da sauran kungiyoyi masu zaman kansu.

Cikinsu kuwa har da kungiyar Lauyoyi, reshen jihar Bauchi, inda a cikin takardarsu suka bada shawarwarin ci gaba da kasancewar jihohi 36 na Nijeriya, da kuma bada shawara ga ‘yan takara ba tattare da tsayawa takara karkashin kowace jam’iyya ba, wannan a duk a cikin Takardar wacce shugaban kungiyar NBA reshen jihar Bauchi, M.M Mai Doki Esk ya gabatar.

A hirarsa da manema labarai, Dakta Waziri Dogo ya bayyana cewa gabatar da wannan bahasin da kuma shirya irin wannan taron ba yanzu ya kamata a ce an gudanar da shi ba. Ya ce ya kamata ne a ce an jima da yin irin wannan taron domin muhimmancin da hakan ke da da shi.

 

Exit mobile version