A. A Masagala" />

Jam’iyyar APC Ta Yi Wa PDP Fintinkau A Zaben Jihar Edo

Daga A. A. Masagala, Benin

A Zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar asabar da ta gabata a jiha Edo jamiyyar APC mai mulkin jihar tayi wa Jmiyyar Adawa ta P.D.P fintinkau azaben  kananan hukumomi da akayi ajihar a ranar asabar 03-03-2018 inda ta lashe zaben kanan hukumomi bakwai.

Sakamakon zaben da hukumar zabe ta jihar (EDSIE) ta fara fitar wa ya nuna da ce wa ita jamiyyar APC  ta samu gagarumar nasara  wanda jamiyyar adawa ta P.D.P  ta nuna fushinta inda ta kaurace wa zaben.

Farfesa Stanley Orobator ya bayyana bayan an kirga kuri’un zaben wanda aka kada Baturen zabe ajihar ya sanar da ce wa Oteh Omoru ne ya yi nasara akaramar hukumar Okoko Edo sai karamar hukumar Obia wanda Destiny Eanabulele ya samu nasara da kuri’u 56,664.

A makwabtan  Obia ta arewa maso gabas kuma Ogbemodia Osaze ne ya yi nasara sai  asauran kananan hukumomin  kamar Kramar hukumar Uhunmwode  da Egor da Owan wadannan duk jamiyyar APC  ta yi nasara awannan zaben da kuri’u da ya ninke na abokan hamayyarta  Irin  S.D.P da sauran.

Kawo lokacin da na hada wannan labarin akwai  sauran kananan hukumomin da hukumar zabe ta jihar din bata fitar da sakamakonsu ba amma bisa ga dukkan alamu dai ita jamiyyar mai mulkin jihar ita ce za ta lashe sauran  zabokan kananan hukumomin gaba daya.

Exit mobile version