Ibrahim Muhammad" />

Jam’iyyar APDA Za Ta Inganta Rayuwar Al’ummar Jihar Kano, Inji Barista Laila Buhari

‘Yar takara majalisar dattawa ta Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APDA, Barista Hajiya Laila Buhari ta bayyana cewa takararta ta neman kawo canji ne don inganta rayuwar al’ummar jihar Kano,duba da irin gazawa da ake samu a bangarori da daman a jagorancinda akewa al’umma.
Barista Laila ta ce ta fahimci yawancin mutane dake siyasa ba al’ummace a gaban su ba yawanci yan jari-hujja ne da suke samun dama a zabesu sai su maida mutane kamar bayi saboda rashin adalci da zalunci da suke musu. Duba da cewa a kowane mataki na kujera akwai albarka dake tare da ita tun daga kan ta shugaban kasa, Gwamna da yan majalisu kundin tsarin mulki ya ba su nauyin da ya rataya akansu, amma yawanci ba wannan ne a gabansu ba sun maida neman tara abin duniya a gabansu fiye da hakkin talakawa.
Ta kara da cewa, a jihar Kano Gwamnoni uku su kadai ke juyata tun da aka shigo siyasar kasar nan daga 1999 har yanzu kuma ba wani kwakkwaran ci gaba. Kwankwaso ya shekara takwas hakama shekarau shi kuma Gwamna na kai yanzu ya shekara takwas yana mataimakin Gwamna yanzu ya shekara hudu a Gwamna yana kokarin yaga ya sake zama a karo na biyu, idan aka lissafa abin da suka samu a mulkin da suka yi da auna yadda Kano take akwai alamar tambaya a kansu.
Barista Hajiya Laila Buhari ta ce, hakama a bangaren wakilcin majalisu tun daga na jiha dana wakilai da na dattawa dukkansu dukkansu suna da rauni, wanda ya kamata ya je ya yi doka sun zama yan amshin shata sunsa ido a kan abin da za a ba su sun gaza yin abin da ya kamata musamman idan shugaba ya yi ba daidai ba sai su sami rauni na daukar mataki, wannan illa ne ga al’umma dan alhakinsu ne kawo dokoki da zai hukunta wanda baiyi daidai ba.
Ta ce, a matsayinta ta mace da Allah yasa musu tausayi da kawo tarbiyya da yin abubuwa da za su tafi kafada-da-kafada da maza wajen inganta rayuwa. Mata suke kulawa da gida abincin da za a ci su dafa su kuma da dawainiyar yara. Ilimin mace yana da muhimmanci kuma yana daga abin da zasu bai wa muhimmanci da inganta lafiya ta gina Asibiti da zai bada kulawa ga mata masu juna biyu, da kuma kokarin su jawo mata cikin siyasa dan kawo kuduri da zai sauya rayuwar mata da matasa a kuma inganta sana’oi da noma wannan zai taimaka ka gina kasar nan ta zama abin sha’awa kamar sauran kasashe da ake zuwa.
Hajiya Laila Buhari ta ce, tana da buri kyautatawa yankin ta Kano ta tsakiya ta bai wa mata jari da horas dasu sana’oi da kuma ilmantar dasu ta yadda za su ci gajiyar ilimin sannan a rika taimakawa masu sana’oi na hannu yanda za su ingantashi ya zama daidai dana kasashen duniya.
Hajiya Laila ta kara da cewa jam’iyyarsu ta APDA tana da dan takarar Gwamna Alhaji Muhammadu Sani Abacha da suke fatan shi zai lashe zabe mai zuwa yanda burin kawo wuta a Kano saboda duk Gwamnoni da aka yi guda uku a Kano sun sha fadar za su gyara Dam a samar da wuta ba wanda ya yi. Muhammadu Abacha zai zo ya yi ya samar da wuta har ma ta sola dan a sami tada masana’antu a inganta harkokin kasuwa ya inganta nomad a lafiya da sauran fannoni na rayuwa.
Ta ce, Kano tana bukatar irin Muhammadu Sani Abacha saboda yana da sabon tunani akansa ba kamar wadanda ke neman takarar Gwamna yanzu bad a taimakon Allah za su hada kai a sami nasara da kawo ci gaba. Tace a baya ta yi PDP da APC kuma kowa yasan yadda Gwamna Ganduje ya yi da takarar mutane ta danniya da aka yi.
Hajiya Laila anyi zalunci kuma dama zalunci Allah baya barin me yinsa suna fata kamar yanda aka yi a 2003 haka za a yi a wannan karon. Da har ma ta hakura da takara sai Allah ya kawo jam’iyyar APDA da take a cikinta tana kuma samun karbuwa a wannan takara, wanda yanzu jam’iyyar APDA ta zama fitacciya a kasar nan kuma sunasa ran kafa Gwamnati a karkashin inuwarta.

Exit mobile version