Jam’iyyar APGA Ta Lashe Kujerar Majalisar Dattawa Na Anambra Ta Tsakiya

Tsohon shugaban jam’iyyar APGA Mista Bictor Umeh ya lashe zaben cike gurbin mazabar majalisar dattijai ta Anambara ta tsakiya da aka gudabar ranar Asabar da ta gabata.

Mista Umeh ya kayar da ‘yan takara 13 a zaben da aka samu karancin fitowar masu jefa kuri’a a tarihin zabe a kasar nan. Mista Umeh ya lashe kuri’u 64,879 a cikin kuri’un 67,000 da aka kada a kananan hukumomi 7 a mazabar, hakan na nuna banbancin kashi 95 tsakaninsa da sauran ‘yantakara.

Dan takarar jam’iyar APC Mista Chris Nigige ne ta zo na biyu da kuri’a 975, yayin da wanda ya zo na uku ke dan kuri’a 116, bayani ya nuna cewa, Mista Nigige ya janye takararsa tun kafin zaben.

Sauran sakamakon zaben ya nuna cewa, jam’iyyar AA ta samu 35, ACD ta samu 33, ADC ta samu 57, GPN ta samu 48, ID ta samu 14 yayin da KOWA ta samu12, LP- ta samu 95, MPPP ta samu 111, NCP ta samu 72, PDP ta samu 5 daga karshe UPP ta samu kuria 55.

Nasarar Umeh’s na zuwa ne bayan kusan shekara 3 da yin zaben gama gari na shekarar 2015 da aka yi a Jihar, a zaben, dan takarar jam’iyar PDP Mista Uche Ekwunife ne ya lashe, amma kotun daukaka kara ta soke zaben a shekarar 2015 sannan ta dakatar da PDP daga takarar zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Bincike ya nuna cewa, kashi 90 na masu zabe suka kaurace wa zaben. Cikin masu ragistar kada kuri’a 745,828 a kananan hukumomi 7 na jiha, masu jefa kuri’a 67,872 kawai suka jefa kuri’unsu. Duk da an sanar da jayewa daga zaben da Ministan Kwadago Mista Nigige ya yi, hukumar zaben ta Sanya sunan sa a jerin masu takara, a haka kuma ya samu kuri’a 975.

Exit mobile version