Hajiya Ummi Tanko Yakasai, ita ce shugabar jam’iyyar Matan Arewa ta shaida wa manema labarai a Kano cewa jam’iyyar matan arewa ba ta goyon bayan kalaman batanci da wasu ‘yan siyasar kasar nan ke yi a kafafen yada labarai na kasar nan ganin ana shirye shiryen tunkaran zabukan 2019.
Jam’iyyar matan arewa zaman lafiya da aikata alhairi take goyon baya a fadin kasar nan. Sannan kuma ‘yan siyasa su fadin alhairi musamman a lokutan yakin neman zabe ba kalaman da za su karo rabuwar al’umma ba.
Malama Ummi Tanko Yakasai ta kara da cewa a matsayin su na iyaye mata, za su ci gaba da yin addu’oin fatan alhairi domin ganin a gudanar da zaben na 2019 lafiya. Duk kuma wanda Allah ya ba shi nasara a kan matsayin da yake nema ya tabbatar ya taimaka wa rayuwar mata da matasan kasar nan.
Alkawuran da yan siyasa suke yi wa al’umma su tabbatar sun cika masu musamman idan suka samu nasaran cin zabe idan kuma suka ki Allah zai tambaye su ranar gobe kiyama.
Da take tsokaci game da rayuwar matasan kasar nan Malama Ummi Tanko, ta ce kasar nan ba za ta ci gaba ba sai da rayuwar matasa nagari wanda al’uma za su yi alfahari da su. Sai da ta koka game da yadda wasu marasa kishin al’umma ke bai wa matasa kwayoyi masu sanya maye wanda suke tayar da hankula musamman a lokacin kamfen sai ta yi kira ga hukumomi da su kara himma wajen kawo karshen wannan dabi’u marasa kyau, su tabbatar sun tsare mutuncin matasa.
Matan da suka fito neman matsayi a cikin jam’iyyun kasar nan kuwa ta yi kira ga matan kasar nan su tabbatar sun kada masu kuri’un su ako wace jam’iyya suka fito, lokaci ya yi a cewar da za a gwada mata domin aga rawar da za su taka.
Daga karshe ta jawo hankulan duk wadanda Allah ya ba su matsayi tun daga kan shugaban kasa, gwamna da sanata da yan majilisar wakilai da sauran su da su tabbatar da shugabanci tsakani ga Allah ba tare da nuna banbanci ba domin yanzu abin da ake bukata a kasar nan shi ne hadin kai da fahimtar juna amma ta na zaton shugaban nin da za’a zaba za su yi adalci ga mata da maza da kuma al’umma gaba daya.