Connect with us

SIYASA

Jam’iyyar NPM Za Ta Bai Wa Wadanda Suka Cancanta Damar Takara –Mustapha Bala

Published

on

An bayyyana cewa, an kafa jam’iyyar “New Progresibe Moberment”NPM ne domin tsaida yan takara da suka cancanta amma basa iya samun damar a tsai da su a cikin sanannun jam’iyyun kasarnan sakamakon siyasar dauki dora data ubangidantaka da ake.Shugaban Jam’iyyar na kasa Mustapha Bala Getso ya bayyana haka a Kano.

Ya ce sun kafa NPM ne duba da yanayinda ake ciki na hana mutane da suka cancanta takara a wasu jam’iyyu sai dai ayi dauki-dora.Da farko ba tunaninsu kafa jam’iyya ba, sai dai duba da yanda jamiyyun suke ba za su bada dama a shiga ayi takara ba komai cancanta saboda dauki-dora kamar yanda jam’iyyun APC da PDP suke,duk yanda wani ya cancanta bazasu bashi dama ba.

Mustapha Bala Getso ya ce jam’iyyar tasu tun kusan shekaru uku da suka gabata aketa fafutukar kafata  sai daga baya suka sami sahalewar hukumar zabe ta kasa tayi musu rijista suka zama jam’iyya zuwa yanzu NPM takai shekara da kafuwa tana da rassa a jihohin kasarna,kuma akwai mutane da suke neman takara a karkashinta a jihohi da dama tun daga kan na Gwamnoni.yan majalisu na jaha dana tarayya da majalisar dattawa.

Ya kara da cewa sun kafa jam’iyyarne domin ta cigaba da wanzuwa ba kamar yanda wasu tsofaffin yan siyasa ke kafa jam’iyyu a jawo mutane a yaudaresu sannan daga baya a jefasu wata da sunan an hade ba,su jam’iyyarsu za ta  cigaba da wanzuwa ko bayan zabe za’a cigaba da ginata dan cigaba da samun karbuwa a tsakanin al’umma.

Ya yi nuni da cewa wasu kuma jam’iyyun ba’a iya cigaba da gudanar dasune sakamakon rashin kudin gudanarwa na al’amuran cigaban jam’iiyun, amma a tsarinsu na NPM zasu cigaba da kokari dan cigaba da gudanarda jam’iyyar takai ga gaci.

Da yake bayani gameda fitowarsa neman takarar Gwamnan jihar Kano a Karkashin Jam’iyyar ta NPM.Mustapha Bala Getso ya ce tun kafin kafa jam’iyyar sunada tunanin matsalolinda suke addabar jihar Kano na rashin samun cigaban al’ummarta yanda yakamata,duba da girmanta amma har yanzu bangaren walwala,lafiya,ilimi,ruwansha da sauran matsalolin rayuwa na addabar mutane.

Me neman takarar tsayawa Gwamnan karkashin NPM ya ce, kullum dan siyasa zancensa zai kawo hanya,ruwa,lafiya da sauransu amma hakan bata samuwa da sun sami dama sai su manta da al’umma.

Sun lura a dawowar  damakwaradiyya  a kasarnan wasu tsirarune keta juya mulkin jihar Kano tsakaninsu.

Mustapha ya ce duba da ganin cewa wannan mulki ba gado bane da kowa ya sauka sai ya kawo wanda yakeso,wannan tasa sukayi tunanin cewa matasa kullum  suke wahala a siyasa ba romo, yakamata ace  sun sami nagartaccen rayuwa,amma babu sai rashin madogara,shi yasa sukaga ya kamata matashi ya fito,duba da irin gwagwarmaya da sukayi a baya.An baiwa kowa dama ya fito a wannan takara a jam’iyyar  da za’ayi zabubbukan fidda gwani na jam’iyya bada jimawa ba.

Dan takara Gwamnan ya ce a dukkan shugabancin jam’iyyunda suke a kasarnan yafi kowa karancin shekaru,kuma jam’iiyar tasu tun bayan Marigayi Malam Aminu Kano   ba’a  sami  wata jam’iyya data samo asali  daga jihar Kano ba,sai wannan jam’iyya ta NPM .Sannan duk a yan takarar Gwamna da suka fito a Kano a jam’iyyu daban-daban ba wanda ya kaishi karancin shekaru.

Shugaban na Jam’iyyar NPM wanda kuma ke neman takarar tsayawa takarar Gwamnan Kano a Karkashinta Mustapha Bala Getso ya yi kira ga jama’a su basu goyon baya dayi musu kyakkyawan zato da tayasu da addu’a na zabin abin dayafi alkhairi a wannan takara da suka fito.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: