Jam’iyyar NRM Ta Yaba Wa Hukumar Zabe

Shugaban jam’iyyar N.R.M ya yaba wa hukumar zabe ta kasa, INEC bisa irin kokarinta na ba jam’iyyu isasshen lokaci su shirya don tunkarar zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Shugaban jam’iyyar Ceton Al’ummar Kasa ‘NRM’ ta kasa, Sanata Sa’idu Dansadau ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da Jaridar LEADERSHIP A Yau dangane da takardar shaidar rajistar da hukumar INEC din ta bayar ga sabbin jam’iyyu 21 a ranar Larabar makon da ya gabata.

Yi wa wadannan sabbin jam’iyyu rajista ya samu amincewar hukumar ne tun daga ranar 14 ga watan Disambar 2017, wanda hakan ya sa ake da jimillan jam’iyyun siyasa masu rajista har guda 68 a fadin Nijeriya.

Sanata Dansadau ya bayyana cewa; “Muna matukar godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya yi wa INEC jagora ta yi cikakke da kuma kyakkyawan bincike game da mu da ma sauran jam’iyyu ta ga cewa mun cancanci a yi mana rajista. Muna farin ciki da wannan, wanda alama ce ta hukumar zabe za ta yi adalci ga zabubbukan nan da za a yi.

“Musamman ma bisa la’akari da cewa an bamu shaidar rajista daidai lokacin da ita hukumar zabe ta kasa INEC, ta bada jadawali na duk al’amuran da za a yi game da zabe har yadda za a yi a gama zaben na shekara ta 2019. Wannan shi ne karo na farko a tarihin Nijeriya, a tarihin siyasar kasar nan inda hukumar zabe ta ba jam’iyyun siyasa isasshen lokaci ta cikakkiyar sanarwa don a shirya, yadda babu wata jam’iyyar siyasa da za ta yi korafi.” In ji shi

Shugaban jam’iyyar ya kara da bayyana cewa wannan sanarwa da hukumar INEC ta yi, ba kawai jam’iyyun siyasa zai taimakawa ba, zai taimakawa jam’an tsaro wurin yin shiri yadda ya kamata. Sannan kuma da wannan sanarwar, hukumar zabe ta yi maganin rashin gaskiyan wasu jam’iyyu ta hanyar yin abin da ya kamata. Ya ce; “Muna kira ga dukkan jam’iyyun siyasa, musamman ma wadanda ke mulki, da ta yiwa hukumar INEC adalci, duk jam’iyyun siyasa su tashi su shirya, ta yadda ba za a zo ana tursasawa hukumar zabe ba a nan gaba, da sunan wai a dage zabe.”

Daga karshe Sanata Dansadau ya bayyana cewa ra’ayin jam’iyyar Ceton Al’umma ‘NRM’ shi ne, duk wata jam’iyya da ta fito ta ce tana so a dage zabe, makiyar Nijeriya ce, mai adawa da dimokradiyya da son yin zalunci.

 

Exit mobile version