Shugabannin jam’iyyar Socialist ta Faransa sun sanar da shirinsu na sanya ginin shalkwatan jam’iyyar a kasuwa, wanda rahotanni ke cewa, za a siyar da shi tsakanin Euro miliyan 40 zuwa miliyan 70.
Ma’ajin jam’iyyar Jean Francois Debat ya ce, daukan matakin na da matukar wahala, amma ya ce, dole ne su yi haka saboda matsalar kudi da jam’iyyar ke fama da ita.
Kazalika, matakin zai bai wa ‘ya‘yan jam’iyyar damar tinkarar makomar siyasarsu a Faransa kamar yadda Debat ya shaida wa manema labarai a birnin Paris.
Wannan dai na zuwa ne bayan mummunan kayin da Jam’iyyar ta sha a zaben shugabancin kasar da na ‘yan majalisu da aka gudanar a cikin watannin Mayu da Junin da suka gabata.