Jam’iyyu 18 Ke Fafutikar Neman Kujerar Gwamnan Anambra – INEC

INEC

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ce, jam’iyyun siyasa 18 ne su ka nuna sha’awarsu ta shiga zaben gwamnan Jihar Anambara da za a yi a ranar 6 ga Nuwamba mai zuwa.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron kwata ta biyu na hukumar da jam’iyyun siyasa wanda aka yi a ranar Alhamis a Abuja.

Yakubu ya ce, dukkan jam’iyyun 18 sun tsara gudanar da zabubbukan su na fidda gwani a bisa jadawalin kwanaki da hukumar ta fitar.

Ya ce, “A kan batun zabubbukan kananan hukumomin Yankin Birnin Tarayya, jam’iyyun siyasa sun gama zabubbukan su na share fage a mazabu 68 da su ka hadu su ka yi shugabannin kananan hukumomin guda shida da kansiloli 62.

“Jimillar jam’iyyu 14 daga cikin 18 sun zabi ‘yan takara 110 na mukaman Shugaba da Mataimakin Shugaba da kuma ‘yan takarar zama kansila su 362.

“Gaba daya dai, jam’iyyu 14 sun fitar da ‘yan takara 472 da za su nemi kujeru 68 a Yankin Babban Birnin Tarayya.

“Akwai zanen taswira da aka yi mai nuna rabe-raben kananan hukumomin a cikin wannan jakar kwalin ta wannan taron da mu ka ba ku.”

Yakubu ya yi kira ga shugabannin jam’iyyun da su rika yin kira ga ‘yan takarar su a zaben gwamnan da na kananan hukumomin da ke Yankin Birnin Tarayya da sauran zabubbukan cike gurbin da ke tafe da su tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce, “Kamar yadda ku ka sani, akwai zabubbukan cike gurbi da na karshen wa’adi da aka shirya gudanarwa kafin Babban Zaben 2023.

“A karshen wannan makon, za a yi zabubbukan cike gurbi guda biyu a Jihar Kaduna, wato na Mazabar Jiha ta Sabon Gari inda jam’iyyu biyar su ka bayar da ‘yan takara, da Jihar Jigawa na Mazabar Tarayya ta Gwaram wanda jam’iyyu goma su ka shiga.

“Mun kammala dukkan shirye-shirye na wadannan  zabubbukan cike gurbin, wanda ya hada da tabbatar da isar muhimman kayan aiki a yau  zuwa mazabun biyu. Zuwa yanzu dai, babu wata hatsaniya a cikin shirye-shiryen.

“Mu na kira a gare ku da ku ja hankalin ‘yan takara da magoya bayan ku da su ci gaba da tabbatar da zaman lumanar da ke akwai yanzu.

“A game da sauran zabubbukan share fage da su ka rage, ina tabbatar maku da cewar da zaran an samu guraben da Kakakin Majalisar Wakilai ya bayyana, za mu fitar da jadawalin lokacin yin su, wato jadawalin lokacin zaben Mazabar Tarayya ta Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato da na Mazabar Tarayya ta Lere da ke Jihar Kaduna.”

 

 

Exit mobile version