Jam’iyyu Da Kungiyoyi Na Kasashe Da Dama Sun Nuna Adawa Da Siyasantar Da Batun Gano Asalin Kwayar Cutar COVID-19

Jam’iyyu

Daga CRI Hausa,

 

A yau ne, jam’iyyu da kungiyoyin zamantakewar al’umma da na masana da yawansu ya zarce 300 daga kasashe da yankuna fiye da 100 na duniya, sun mika wata hadaddiyar sanarwa ga ofishin sakatariya na hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, inda suka jaddada cewa, yayin da ake tinkarar barazanar da cutar COVID-19 ta kawowa lafiyar dan Adam, akwai bukatar kasashen duniya da su kara yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar, tare da yin kira ga hukumar WHO da ta gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19 a duniya cikin adalci maimakon siyasantar da batun.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, aikin gano asalin kwayar cutar COVID-19, nauyi ne na kasashen duniya, shawarar aikin gano asalin kwayar cutar COVID-19 a mataki na biyu, da ofishin sakatariya na hukumar WHO ya gabatar, bai dace da kudurin da aka tsaida a gun babban taron hukumar, kana kasashe membobin hukumar, ba su tattauna batun ba, kana shirin bai shaida sabon sakamakon nazarin aikin gano asalin kwayar cutar a duniya ba, don haka shirin ba zai taimaka ga hadin gwiwa kan binciken gano asalin kwayar cutar a fadin duniya yadda ya kamata ba. (Zainab)

Exit mobile version