Abdullahi Muhammad Sheka" />

Jam’iyyun Adawa Da Gamayyar Kungiyoyin Sa-kai Sun Taya Ganduje Murna

Kwanaki kadan bayan Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya aika wa da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahu Umar Ganduje sakon taya murna bisa nasarar da ya samu a Kotun sauraron korafe-korafen zabe, su ma Jam’iyyun adawa sama 50 tare da sauran gamayyar Kungiyoyin Sa-kai, karkashin inuwar (APCAP) sun taya Gwamnan murnar samun wannan nasara.
Sakon haka na kunshe ne cikin wata wasika da aka aika wa Gwamna Ganduje a ranar Juma’a 4 ga watan Oktoban shekarar 2019, wadda jagoran kungiyoyin Basarake Benjamin Aturu Dogo da Bello Sanin Kwalla suka rattabawa hannu. Gamayyar Jam’iyyun adawar tare da hadin guiwar
Kungiyoyin Sa-kan ne suka tabbatar da haka, kamar yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana.”
Haka zalika, sun sake tabbatar da cewa, dan takarar da ya yiwa Jam’iyyar PDP takara Abba Kabir Yusif, yana da dukkanin damar daukaka kara akan hukuncin da aka yanke. Sannan sun sake fayyace cewa, wannan nasara da Gwamna Ganduje ya samu wata ‘yar manuniya ce da ke nuna kwarewa wajen gudanar da harkokin shari’a, saboda haka, ko dai su daukaka kara ko kuma su hakura labarin dai haka zai kasance ba tare da samun wani sauyi ba har zuwa shekara 2023.”
Har ila yau, wadannan kungiyoyi sun fayyace komai da komai ga mai girma Gwamna cewa, a bayyane yake ga kowa, ba dole sai masanin shari’a ne zai fahimci gaskiyar wannan al’amari ba, a lokacin da Jam’iyyar PDP ke gabatar da shaidunta cewa ta yi, wannan wata da ma ce da za ta bayyana yadda Nijeriya ta gudanar da ingantaccen zabe.
A cewar kungiyoyin, shaidun sun bayyana a gare mu yadda masu adawa da nasarar Gwamna Ganduje, suka kasa kare abinda suke korafi akansa. Hukuncin kansa wata ‘yan manuniya ce ga Gwamna Ganduje, wadda ke tabbatar da kyakkyawar halayya ga masu adawa da hukuncin Kotun. “Saboda haka bayan yanke hukuncin, babban abinda ka fi mayar da hankali akansa shi ne
jaddada aniyarka ta samar da ingantaciyar lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano.”
Wani bangare na wasikar ya kara tunawa jama’a cewa, daukaka karar da Jam’iyyar PDP ke niyyar yi  zai kara bayyana gazawar jam’iyyun adawa, wanda suka hakikance zai kara jefa Jam’iyyar PDP cikin rashin tabbas da kuma rashin tsari a zaben shekara ta 2023 mai zuwa a kasar nan.
“Kasancewar mu gamayyar Jam’iyyun adawa da kuma wasu kungiyoyin Sa-kai, mun taka muhimmiyar rawa a lokacin zaben gwamna da ya gudana, mun hakikance duk wani mataki da Jam’iyyar PDP za ta dauka nan gaba, bata lokaci ne kai wanda a karshe zai kara rage kimar Jam’iyyar a dukkanin matakai musamman a Jihar Kano.
“Domin kara nuna farin cikinmu, musamman yadda aka nuna dattako bayan yanke hukunci wanda Jam’iyya mai mulki ta APC ta nuna a lokacin gudanar da murnar samun nasara, muna kara tabbatar wa da ‘yan siyasar Nijeriya cewa, Jihar Kano ta kama hanyar taka babban matsayi a tsarin fahimtar demokaradiya. Saboda tabbacin da muke da shi cewa, ba a samu wata barna
daga bangaren magoya bayan Jam’iyyar APC ba.”
Saboda haka, muke kira ga dukkanin Jam’iyyun adawa da suka hada karfi wajen gabatar da wannan sakon taya murna, su fahimci cewa bukatar sake dawowarsu akan kujerar mulkin Kano da kasa baki-daya, akwai bukatar sake fasalin Jam’iyyun domin fuskantar Jam’iyya mai mulki ta APC.
A kokarin Gwamna Ganduje na daidaita al’amura wanda zai samar da gwamnatin kowa da kowa, wasikar ta jadadda cewa, “hakan wani abu ne da zai kara rage karfin Jam’iyyun adawa, amma dai har yanzu muna da tabbacin Gwamnatin Ganduje, na da kyakkyawan fata ga al’ummar Jihar Kano.
Haka kuma, za mu cigaba da bibiyar dukkanin wani mataki na gwamnati domin kara maka karfin guiwa wajen gudanar da kyakkyawar jagoranci.” Kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.

Exit mobile version