Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, goyon bayan da jam’iyyar Conserbatibe ta shugabar gwamnatin Jamus ke da shi ya ragu, yayin da kashi daya cikin uku na al’ummar kasar suka gaza yanke shawara kan wanda za su kada wa kuri’a a zaben game-gari da za a gudanar cikin wannan watan.
Sakamakon wannan kuri’ar ta jin ra’ayin jama’a da aka fitar a wanan Jumma’a, ya dada haifar da fargaba game da irin hadakar da za ta kai ga gaci a zaben game-gari da za a gudanar a ranar 24 ga wannan wata na Satumba a Jamus.
Kuri’ar jin ra’ayin ta nuna cewa, goyon bayan da jam’iyyar Conserbatibe mai ra’ayin rikau ta shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ya ragu da kashi 36 cikin 100.
Sai dai wasu na ganin hakan ba zai hana jam’iyyar samun rinjaye a Majalisar dokokin kasar ba.
Su kuma jam’iyyun FDP ta ‘yan Democrat da AFD ta masu adawa da bakin haure kowannesu na da kashi 10-10 wajen samun magoya baya.
Kuri’ar wadda aka fara gudanarwa daga 12 zuwa 14 ga watan Satumba ta kuma nuna cewa, har yanzu kashi 39 na Jamusawa ba su yanke shawarar wanda za su kadawa kuri’a ba.