A kwanan baya ne, Shuagaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nada Manyan Hafsoshin Tsaron Kasar, inda hakan ya nuna wata alama, na kokarin da Gwamnatinsa ke kan yi, na magance kalubalen rashin tsaro, da ya yi wa kasar daurin Demon Minta.
Akasarin masu ruwa da tsaki a kasar, sun yi maraba da wannan nadin, duba da cewa, akwi matukar bukatar sojin kasr su tashi haikan, domin kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga daji da masu sace mutane domin karbar kudin fansa da magance rikice-rikecen da suka shafia addini da ke hair da hallaka ‘yan kasar da kuma aikata, saurn manyan laifuka.
- An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu
- NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna
A ra’ayin wannan Jaridar mun yi tuanin cewa, wannan nadin na su, ya nuna cewa, akwai jan aiki a gaban manyan hafshoshin tsaron kasar, kuma dole su tashi tsaye, domin sauke nauyin da aka dora masu.
Aikin na sun a farko shi, samar da daidaito a cikin aikin na soji, musamman wajen kawar da rarrabuwar kawuna a gidan soji, wanda idan suka magance hakan, zai kara dawo da karasashin dakarun sojin da kuma kawar da duk wani banbanci, a tsakaninsu.
Muna sane da irin gagarumain namijin kokari da sadaukar da kan da dakarun ke ci gaba da yi a fagen daga, musamman domin magance kalubalen rashin tsaro da ke ci gaba da addabar kasar.
A bisa wannan dalilin, ya kuma zama waji, manyan hafsohin tsaron su mayar da hankali, wajen ingnata jin dadi da walwalar dakarun sojin, musamman duba da cewa, manyan hafsoshin tsaron, su ba baki ne, kan wadannan kalubalen ba, domin kuwa kafin nada su, a baya an nada su kan makamai da ban da ban.
Kwarewar da kuma ilimin da suke da shi, a aikin soji, abu ne da zai taimaka masu wajen sauke nauyin da aka dora masu.
Abu na biyu shi ne, akwai bukatar a tsakaninsu, su hada karfi da karfe, domin su samu nasarar tunkarar aikin da ke a gabasu na tabbatar da tsaro a kasar, ba wai su rinka yi aiki, a daidaikunsu ba.
Kazalika, dole na rundunar sojin sama ta taimaka wa rundunar soji na kasa da kuma na ruwa, a yayin duka wani farmaki, tare da kuma yin musayar bayanai, a tsakansu.
Na ukun shi ne, dole ne su mayar da hankali kan samar dabaru, yayin gudanar da ayyukansu, musamman duba da irin sarkakiyar da ke tattare da yanayin kalubalen rashin tsaron kasar, misali duba da irin salon ayyukan ‘yan bindiga daji da masu garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan ta’adda, na kai hare –hare, wanda a yanayi irin wannan akwai matukar a dauki dabarun magance wannan barazanar ta su.
Yakar ta ‘yan bindiga daji da masu garkuwa da mutane da kuma masu aikata manyan laifuka, ya zarce ace manyan hafsoshin tsaro ne kadai za su yi hakan, domin kuwa, akwai kuma bukatar su tabbatar da sun samu goyon bayan alummar gari, musamman ta hanyar samun bayanan sirri.
Bugu da kari, na hudun shi ne, su tabbatar da dakarunsu na kai farmaki ta kasa duba da cewa, akasarin kalubalen rashin rashin tsaron ya ta’allaka ne na kasa, musamman duba da cewa maboyar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga daji, a kan doron kasa suke.
Dole ne manyan hafsoshin tsaron su sanya a zuciyarsu na cewa, su masu yin biyayya ne, ga kundun tsarin mulkin kasar kuma dole ne su kare su tabbatar da sun kare dorewar mulkin dimokaradiyyar kasar.
Kazalika, ya zama wajbi, a tantace a tsakanin ayyukan soji na kuma na siyasa.
A saboda haka ne, ba ma goyon bayan soji yin kutse a cikin batun abinda ya shafi fanin siyasa, musamman duba da cewa, kasashen da soji suka shiga cikin lamarin siyasa, sun kasance, ba su ji dadi ba, kuma bai kamata Nijeriya ta kasance a cikin jerin irin wadannan kasashen ba.
Wannan Jaridar na shawartar ‘yan siyasar kasar nan, kar su kutsa kansu kan batun da ya shafi lamuran ayyukan sojin kasar, musamman gwamnonin jihohin kasar, musamman duba da cewa, mun lura da irin wannan shishigin na wasu ‘yan siyasar kasar inda suke bayyana gazawar da sojin kasar ke yi, na tabbatar da tsaro a kasar.













