A ranar ranar Lahadin data gabata aka yi wa Lionel Messi jan kati a wasan karshe da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Athletic Bilbao na gasar Spanish Super Cup inda Athletico din ta lashe kuma na uku kenan jumulla.
Athletic Bilbao ta yi nasara ne da ci 3-2, bayan karin lokaci da suka tashi 1-1, kuma Athletic ce ta fitar da Real Madrid a wasan daf da karshe da ci 2-1 abinda yasa ake ganin kungiyar tayi gagarumar bajinta na bige manyan kungiyoyin Real Madrid da Barcelona a gasa guda daya.
Wannan ne karon farko da aka bai wa Messi jan kati a Barcelona a wasanni 753 da ya yi a kungiyar a dukkan fafatawa koda yake shi ne karo na uku da dan kwallon ya karbi jan kati a tarihin sana’arsa ta kwallon kafa.
‘Yan lokuta kafin nasarar Bilbao, anga Messi na wurga hanu ga Asier Billalibre, wanda ya ci kwallo a mintuna 90 da ya hanawa Barcelona nasarar kwallaye biyu da Annonie Greizman ya zura a ragar Bilbao, abin da yasa aka tsawaita lokacin wasa, kuma Inaka William ya ciwa Bilbao kwallo ta 3 da ya basu nasarar lashe kofin.
Messi, mai shekara 33 ya fara karbar jan kati a wasan da tawagarsa ta Argentina ta yi da Hungary a shekarar 2005 sannan ya kuma karbi na biyu a gasar Copa America wasan neman mataki na uku a shekarar 2019 a wasa tsakanin Argentina da Chile.
Ana ganin watakila a dakatar da Messi buga a kalla wasanni hudu da zai iya shafar La Liga da sauran kofunan gaba da ake buga wa a Spaniya wanda hakan ba karamar matsala Barcelona zata fuskanta ba musamman ma idan aka duba halin da kungiyar take ciki a wannan kakar.
Kawo yanzu Messi shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Spaniya mai kwallo 11 a raga, kuma Barcelona tana ta uku a teburin gasar bana ta La Liga ya yinda Real Madrid take a mataki na biyu sai Atletico Madrid a mataki na daya.