Abba Ibrahim Wada" />

Jana’izar Siyasar ‘Yan Majalisar Nijeriya Na Yanzu A 2019 (4)

Har yanzu dai muna kan bayani game da rashin yin Katabus a aikin Majalisa da rashin samun kyakkyawan wakilcin al’umma a majalisar daga galibin mutanen da aka tabbatar da cewa an zabe su ne domin su tabbatar da yi wa al’umma wakilci nagari a cikin gwamnati.

Wancan Gidan Jarida (Daily Trust) da nake tsokaci kan abin da ya ruwaito, ya dora bayanin nasa ne kamar haka, “Babban aikin wadannan ‘Yan Majalisa kamar yadda aka fayyace a cikin sashen Doka na 4 (1-9) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na Shekarar 1999, shi ne, su kirkiri Dokokin da za su wanzar da zaman lafiya da bin doka da oda gami da samun ingantacciyar Gwamnati a Tarayyar Najeriya ko ga wani yanki na Kasar…”

Jaridar ta cigaba da cewa, “A fili ne yake cewa, sikelin da ake gane kwazon wadannan ‘Yan Majalisa shi ne, ta hanyar la’akari da kokarinsu na daukar nauyin Kudurin Doka (bill sponsorship), jagorantar al’amura bisa doka (obersight), gudunmuwar da Dan Majalisa ke badawa wajen tafka muhawara a dandamalin majalisar, a game da wasu Kudurori (motions) da Kudurin Doka (bill) da ma sauran ababen da Majalisa ke da ruwa-da-tsaki ciki (other legislatibe interbention), wadanda aka gabatar a gaban ZAUREN MAJALISAR yayinda take zama”.

Ya tabbata cewa, “Cikin Watan takwas na Shekarar da ta gabata (August, 2017) da aka nazarci adadin wadanda suka dauki nauyin gabatar da Kudurin Doka (bill) a Majalisa, sai binciken ya nuna, akwai SANATOCI kimanin goma sha-shida (16) wadanda ba su taba cimma nasarar gabatar da irin wancan kudurin doka ba, alhali a lokacin da aka yi waccan kididdiga, sun shafe kimanin Watanni 26 ne da rantsar da su a Majalisar (suna zaman-dabaro)”

Da aka waiwayi zauren ‘Yan Majalisar Wakilai kuwa, sai aka iske cewa, “ ‘Yan Majalisar Wakilai 160 ne cikin 360 suka sami damar gabatar da kudirin doka guda-guda, cikin Shekarar da ta gabata ta 2017”

Tsokaci;

Me ake nufi da Kudirin Doka (bill)?;

Da farko ya kamata mu sani cewa, daukacin dokoki na fara rayuwarsu ne a matsayin BILL a nan Zauren ‘Yan Majalisa.

Ma’anar Bill;

Bill ya kasance, “Rubutaccen kudirin doka ne da ake gabatar da shi a zauren majalisa don neman sahalewarsu gabanin ya zama doka cikakka”

Bill kan zama Doka ne cikakkiya, bayan samun sahalewa daga mafiya rinjayen “Yan Majalisu.

Kashe-kashen Bill;

A mabanbantan wurare, za a ga cewa yayin fayyace gida-gida ko aji-aji na bill da ake da shi, a kan gabatar da ko dai iri hudu ne ko kuwa iri uku;

i-Public bill

ii-Money bill

iii-Pribate member’s bill, sannan,

ibPribate bill

Wasu masanan, kan gabatar da rabe-raben bill din ne kamar haka;

i-Public bill

ii-Pribate member’s bill, sai

iii-Pribate bill

 

Ba matsala ba ne cikin gabatar da kashe-kashen bill din a matsayin ya kasu gida uku ne ko hudu, tun da wajen fadada ma’anar kowannensu, za a ga duka abu guda ne ake magana a kai.

i-Ma’anar Pubic bill;

Amsa; A na fassara wannan bill ne da, “Wani kudirin doka ne da ya shafi lamarin rayuwar daukacin al’umar Kasa. Sannan irin wannan kudirin doka za a ga cewa bangaren zartarwa ne na gwamnati irin su MINISTA ke da alhakin gabatar da shi a zauren majalisa”. Misali, kamar sha’anin wutar lantarki, lafiya, tsaro da makamantansu, ai za a ga wasu ababe ne da suka shafi daukacin al’umar Kasa.

ii-Ma’anar Pribate member’s bill;

Amsa; Wannan bill na nufin, “Kudirin doka ne da shi ma ya shafi rayuwar al’umar Kasa bakidaya, sai dai shi wannan kudirin doka, za a ga cewa Dan Majalisa ne kawai ke da alhakin gabatar da shi a zauren majalisa, ba bangaren zartarwa ne na gwamnati ba”. Sannan,

iii-Ma’anar Pribate bill;

Amsa; ma’anar wannan bill shi ne, “Wani kudirin doka ne da kawai ya shafi wani karamin yanki na al’umar Kasa. Kamar wata karamar hukuma misali. Sannan wannan kudirin doka za a ga cewa al’umar da abin ya shafa ne ke gabatar da kudirin dokar a zauren majalisa”.

Za mu kwana a nan sai Allah ya kai mu mako nag aba za mu dora daga inda muka tsaya. A tare mu cikin Yardar Mahalicci.

 

Exit mobile version