Jana’izar Sojojin Da Suka Mutu A Hatsarin Jirgi Ta Gudana Cikin Alhini

Daga Khalid Idris Doya

An yi jana’izar dakarun rundunar sojojin sama matuka jirgi su bakwai da suka mutu a ranar Lahadi, sakamakon hatsarin jirgin saman da ya rutsa da su, a makabartar sojoji da ke Abuja, cikin alhini tare da cikakkiyar karramawa.
Sojoji bakwai din sun hada da Flight Lieutenant Haruna Gadzama (Captain), Flight Lieutenant Henry Piyo (Co-Pilot), Flying Officer Michael Okpara (Airborne Tactical Obserbation System (ATOS Specialist).
Sauran sun hada da Warrant Officer Bassey Etim (ATOS Specialist), Flight Sergeant Olasunkanmi Olawunmi (ATOS Specialist), Sergeant Ugochukwu Oluka (ATOS Specialist) da kuma Aircraftman Adewale Johnson (Onboard Technician).
Wakilan mamatan ne suka karbi tagomashin karramawar daga babban hafsan matuka jiragen sama, Air bice Marshal Oladayo
Amao, kazalika da aza furanin dajewa, hadi da harba harsashi ban girma daga majibanta rufe gawawarwakin.
Baban Hafsan mayaka Saman ya kasa jure zuciyar sa inda hawaye suka bayyana zuba daga idanuwan sa a yayin da yake bayyana jimamin sa.

Mukaddashin Hafsan Mayaka Amao, wanda shi ma ya kasa shawo zuciyar sa, ya barke da hawaye daga idanuwan sa, inda aka dauki lokaci hawaye na zuwa daga fuskarsa, yayin da yake bayyana jimami a wajen bikin bunne gawarwakin, tare da bayyana mamatan a matsayin fitattun hafsoshi wadanda suka sadaukar wajen ganin an samu kyautata kasar nan, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rigamu gidan gaskiya sakamakon wannan hatsarin.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin bison sun hada da gwamnan jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi; ministan mata, Dame Pauline Tallen; ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed; shugabanin hukumomin tsaro, tsoffi da manyan jami’an soji da ke aiki a halin yanzu, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sojin sama, tare da wasu manyan kusoshi a Nijeriya.

Exit mobile version