Daga Muhammad Maitela, Damaturu
A ci gaba da ziyarar aiki a arewa maso gabas, shugaban rundunar sojojin Nijeriya (COAS), Lt. Janar Ibrahim Attahiru ya kai wa shalkwatar sojojin Nijeriya ziyarar karfafa gwiwa, na runduna ta biyu da ke karkashin Lafiya Dole a Damaturu ranar Lahadi.
A jawabin da ya gabatar wa sojojin, Janar Attahiru ya bayyana cewa; “Mun zo jihar Yobe ne mu ziyarci wadannan bangarori na shalkwatar sojoji, domin mu hadu daku, kana mu bayyana muku dangane da abubuwan da suka hau kanmu. Sannan da isar da gaisuwar ban-girma daga shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawan Nijeriya, wanda mun shaida masa kuma da masaniyar sa a dukan kokarin da kuke yi.
“Har wala yau kuma, a kashin kaina, a matsayina na shugaban rundunar sojojin Nijeriya, na ziyarce ku a nan ne domin tattaunawa don gano kalubalen da kuke fuskanta tare da baku tabbacin daukar matakan magance su, wanda hakan zai taimaka wajen kara muku karsashi da samun damar gudanar da aikin ku cikin shauki da alfahari a matsayin ku na zaratan sojojin Nijeriya.
“Haka kuma, ina mai jinjina muku, domin kwamandojin ku sun shaida min irin kokarin da kuka yi na bai-daya a karkashin ‘Tura Ta kai Bango’ dangane da yadda kuka fatattaki mayakan Boko Haram, wanda bisa ga wannan mu na alfahari daku kuma na yi imani a samamen da za a gudanar nan gaba za ku nuna kwazo fiye da na baya.”
Bugu da kari, ya ce, “Sannan kuma ina da yakinin cewa za ku fita bakin daga, ku fatattake su da karfin kunda tare da gama wa da yan ta’adda baki daya, kana kuma mun fahimci dukan kalubalen da kuke fuskanta kuma zan daukin shawo kan baki dayan wadannan matsaloli naku, na kara jinjina muku.”
A hannu guda kuma, a ganawar sa da manema labarai, jim kadan da yi wa sojojin jawabi, babban Hafsan sojojin, Laftanar Janar Attahiru ya bayyana makasudin wannan ziyarar aiki ga baki dayan wadannan rundunonin sojojin a yankin, inda ya fara da shalkwatar tsara dabarun yaki ta Lafiya Dole.
Yayin da kuma ya bai wa sojojin da ke aikin samar da tsaro a yankin tabbacin shawo kan matsalolin su tare da karfafa musu gwiwa domin samun karsashin tunkarar yaki da Boko Haram gadan-gadan don kawo karshe matsalar tsaron.