Mustapha Abdullahi">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Janar Kukasheka Ya Zama Sarkin Yakin Ketaren Katsina

by Mustapha Abdullahi
February 2, 2021
in LABARAI
1 min read
Janar Kukasheka Ya Zama Sarkin Yakin Ketaren Katsina
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kanwan Katsina, kuma Hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello kankara ya bayar da sarautar ‘Sarkin Yakin Ketare’ ga Tsohon Kakakin rundunar sojan Nijeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya).
Baya nan da muke samu sun bayyana cewa Kukasheka na cikin muhimman  mutanen da suka samu Sarauta daban-daban bayan da mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabor Usman ya amince da a nada su.
Wannan bayar da sarautun, wani bangare ne domin bikin murnar cika shekaru Ashirin (20) da nadin da Mai martaba Sarkin Katsina ya yi wa Alhaji Usman Bello kankara, wanda ya kasance babban jami’in Hukumar kwastan ne ta kasa kafin ba shi Sarautar.
Sauran da aka ba sarautar, sun hada da Awwal Usaman Bello kankara a matsayin Ciroman Kanwa; Alhaji Ibrahim Sama’ila, Sarkin Fada; Bishir Sama’ila, Sallama; Alhaji Mannir Abubakar, Garkuwa; Lawal Abnas, Zanna; Munauwar Ibrahim, Tafida; Abdulrahman Bello, Wazirin ayyuka; Usman Yusuf, Muhti da kuma Musa Isma’il Mani a matsayin Sarkin Waka.
Sauran su ne, Alhaji Rabi’u Wada Ketare, Hasken Fada; Mohammed Usman Bello, Sarkin Hawa; Isa Mohammed da ke aiki a Hukumar kula da ilimi bai-daya ta Jihar Katsina a matsayin Talba; Labaran Bello kankara a matsayin Wambai; Alhaji Sule Ketare, Waziri; sai Malam Imrana kankara Khadimul Islam; Sanusi Labo, Ajiyan Kanwa da kuma Hashimu Jobe a matsayin Sardauna.
Kanwan na Katsina, ya kuma bukaci wadanda aka ba wannan sarautu da su ci gaba da taimaka wa masarautar Ketare, karamar Hukumar kankara, Jihar Katsina da Nijeriya baki daya. Kamar yadda ya ce an ba su wannan sarauta ne sakamakon irin gudumawar da suke bayarwa wajen ci gaban masarautar da kuma yankin na Ketare baki daya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Rashin Bude Filin Jiragen Saman Kano Ya Jefa Mu Matsala – ’Yan Kasuwa

Next Post

Tattaunawa Ce Babbar Hanyar Magance Matsalar Tsaron Nijeriya – Bayero Fullo

RelatedPosts

Neman Buhari Ya Sauka: Mun Cafke Tsohon Hadimin Ganduje -DSS

Neman Buhari Ya Sauka: Mun Cafke Tsohon Hadimin Ganduje -DSS

by Mustapha Abdullahi
10 hours ago
0

Hukumar Tsaro Ta Farin kaya (DSS) Ta Bayyana cewa tana...

Dan Majalisar Tarayya Ya Sabunta Katin Jam’iyyar APC A Funtuwa

Dan Majalisar Tarayya Ya Sabunta Katin Jam’iyyar APC A Funtuwa

by Mustapha Abdullahi
20 hours ago
0

Daga Hussaini Yero, Funtua  Dan majalisar Tarayya me wakiltar mazabar...

Sace Daliban Zamfara: Sarkin Musulmi Da Gwamna Tambuwal Sun Kai Ziyarar Jaje

Sace Daliban Zamfara: Sarkin Musulmi Da Gwamna Tambuwal Sun Kai Ziyarar Jaje

by Mustapha Abdullahi
21 hours ago
0

Daga Hussaini Yero, kasa da awa goma sha biyu da...

Next Post
Tattaunawa Ce Babbar Hanyar Magance Matsalar Tsaron Nijeriya – Bayero Fullo

Tattaunawa Ce Babbar Hanyar Magance Matsalar Tsaron Nijeriya – Bayero Fullo

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version