Janareto 32,800 Ke Bai Wa ICT Wutar Lantarki, Cewar Gwamnatin Tarayya

Tattalin Arzikin Nijeriya

A ranar Talata ce, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, samar da wutar lantarki ya zama babban matsala wajen bunkasa fasahar sadarwa (ICT), idan a yanzu haka sama da janareto 32,800 ake amfani da su a Nijeriya wajen bai wa cibiyoyin ICT wutar lantarki. Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin ta hanyar zamani, Isa Pantami shi ya bayyana hakan a Abuja wajen kaddamar da ayyukan cibiyoyin fasahar sadarwa guda 11 da ma’aikatarsa ta gudanar da jihohi daban-daban da ke cikin kasar nan. Pantami ya bayyana hakan ne lokacin da yake mayar da martini ga ministan harkokin waje, Rauf Aregbesola a kan bukatar fadada ICT a Nijeriya domin magance matsalar tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki. Ya bayyana manyan kalubalan da ake fuskanta guda biyu a fannin wanda suka hada da bin hanyoyin da suka dace da matsalolin wutar lantarki.

Ya ce, “bisa matsalolin da ake fuskanta a yanzu musamman ma na harkokin sadarwa, ina tunanin wannan ba karabin abin lura ba ne.
“Bisa kokarin da shugaban kasa ya yin a magance matsalar bin hanyar da ta dace wanda muka yi kokarin dakilewa, ya kara farfado da harkokin fasahar sadarwa a Nijeriya.
“Babban matsalar da ake fusakanta a yanzu dai shi ne, abubuwan da suke rage ingancin ayyukan a Nijeriya, idan aka samu kayayyakin more raywa to za a iya magance lamarin. Ina mai neman afuwan abokaina da suke wajen nan musamman ma ministan wutar lantarki, domin babban matsalarmu shi ne wutar lantarki wanda ya fi karfin kulawarmu.
“A yau a Nijeriya mafi yawancin kayayyakin aikinmu suna amfani da janareta ne wajen samar da wutar lantarki, sakamakon karancin wutar lantarki da ake samu.
“Bisa rahoton da nake samu, muna da sama da janareto guda 32,800 a fadin kasar nan da ke bai wa kayayyakin aikinmu wutar lantarki,” in ji Pantami.
Ministan sadarwa ya yaba wa karamin ministan wutar lantarki, Goddy Jedy-Agba, wanda shi ma ya halacce wannan taro, bisa yadda yake kokarin samar da wutar lantarki a Nijeriya. Pantami ya kara da cewa, gwamnati ne ke da ikon samar da tsaro a dukkan cibiyoyin ICT da ke kasar nan. Ya ce, wannan zai taimaka wajen rage kashe kudade na aiwatarwa. Ya ci gaba da cewa, sun yi kokari da yawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan ta hanyyar zamani. Ministan ya bayyana cewa, game da wadannan cibiyoyin ICT guda 11 da aka kaddamar da ayyukansu a yanzu haka, za su taimaka wajen farfado da tattalin arziki da inganta tsaro da kuma samar da ayyukan yi a cikin kasar nan.
Ayyukan dai sun hada da cibiyar tattaunawa cikin gaggawa da ke Ilorin Jihar Kwara da cibiyar tattaunawa cikin gaggawa da ke Kalaba cikin Jihar Kuros Ribas da cibiyar ilmantar da ‘yan makaranta da ke GDSS cikin Jihar Gombe da cibiyar ilmantarwa na manyan makarantu da ke jami’ar Delta a Abraka da kuma cibiyar jarabawa da ke Maiduguri cikin Jihar Borno.
Sauran dai sun hada da cibiyar kirkiro bayanan kimiyya da fasaha da ke jami’ar Jihar Kogi da cibiyar gina fasahar sadarwa da ke kwalejin ilimi cikin Jihar Jigawa da kuma cibiyar gina bayanan kimiyya da fasaha da ke FUTO ta Jihar Imo. Sauran ayyukan dai sun hada da cibiyar yada bayanai a kan lafiya da ke Abubakar Tafawa Balewa cikin Jihar Bauchi da sabon ofishin sadarwa da ke Jihar Delta da kuma cibiyar canza sakonni da ke Mbiama cikin Jihar Bayelsa.
Da ya ke gabatar da jawabi a wajen taron, ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa, wannan gwamnatin ta yi kokari sosai amma a bari ‘yan Nijeriya su ga abin da ta yi. Ya kara da cewa, bunkasa kimiyya da fasaha ya na sa ayyukan gwamnati su kasance cikin sauri da kuma sauki.

Exit mobile version