Abdullahi Muhammad Sheka" />

Jaridar Business Today Za Ta Karrama Ganduje A Fannin Noma Da Lafiya

Bisa samun nasarar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi a bangaren harkokin noma da kuma na lafiya, fitacciyar Jaridar harkokin Kasuwanci (Business Day), bayan gudanar da dogon bincike tsakanin gwamnonin Nijeriya 36 ciki har da Abuja, ta zabi Ganduje a matsayin wanda za ta karrama da lambar yabo ta gwamnan da ya yi wa sauran gwamnoni fintinkau tare da samun nasara a bangaren harkokin noma da cigaban harkokin lafiya na Shekarar 2019.
A jerin shirye-shiryen da aka yi wa lakabi da ‘Karramawa akan Gasar Shekara ta 2019 da kyakkyawan jagoranci’, wanda aka tsara gudanarwa a ranar Alhamis 24 ga watan Oktoban shekarar 2109, wanda za a gudanar a dakin taro na Otal din Transcorp da ke Abuja. Kazalika, za a karrama Gwamnan Ganduje da manyan lambobin yabo har guda biyu a lokaci guda.
Wannan sako na kushe ne cikin wasikar da aka aikawa da Gwamna Ganduje, mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Oktoban shekarar 2019, wanda mawalalfin Jaridar Business Today Mista Frank Aigbogun, ya rattabawa hannu.
Wasikar ta ce, “Kwamitin Gasar karramawa ga gwamnan da ya fi sauran gwamnonin Nijeriya ta fuskar kyakkyawan jagoranci, na farin cikin sanar da mai girma gwaman cewa, an zabe shi a matsayin gwamnan da zarta sauran Gwamnonin Kasar nan, ta fuskar samun nasara a bangaren noma da kuma cigaban harkokin lafiya.
Haka zalika, Kwamitin shirya wannan gasa zai yi amfani da wannan dama domin taya mai girma Gwamna murna bisa nasarorin da ya cimma.”
Jaridar ta tabbatar da cewa, Kwamitin bayar da Lambar karramawar ya samu tagomashin fitattun ‘yan Nijeriya da suka duba aikin Kwamitin akan kyawawar manufofi da aikace-aikacen da gwamnan ya aiwatar a Jihar Kano, musamman ta fuskar harkokin tattalin arziki da ilimi, ayyukan raya kasa, lafiya, noma, yaki da fatara da kuma cigaban harkokin Karkara, tun bayan zuwan Gwamna Ganduje.
A cewar Jaridar, “wannan gagarumar nasara da ake gani wadda ke tabbatar da kyakkyawan shirin sake fasalin Kano, kyakkyawan yanayin Kasuwanci, samar da karin damammaki da kuma ciyar da harkokin tattalin arziki gaba, wanda Gwamna Ganduje ya kirkira kuma ake aiwatar da su.
“Babu shakka, wannan wani tsari ne da ake fatan nuna nasarorin da Gwamna Ganduje ya samu ga daukacin duniya, wanda Jaridar Business Day ta bayyana wasu hanyoyi domin nuna farin ciki da nasarori wanda ya haifar da samun wannan lambar yabo.”
Ta ci gaba da cewa, “daga cikin abubuwan da za a gudanar domin nuna murnar wadannan nasarori, za mu yi amfani da hanyoyin sadarwa na cikin gida kamar jaridarmu ta yau da kullum, Jaridar karshen mako, kafar sadarwa ta yanar gizo, domin tallata nasarorin gwamnatinka ga duniya bakidaya.” Kamar Yadda Babban Darkatan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.

Exit mobile version