Jaridar Washington Post: Jami’iyyar Republican Na Maimaita Tarihin Ta Na Dora Laifi Kan Wasu

Daga CRI Hausa,

Jairdar “Washington Post” da ake wallafawa a Amurka, ta fitar da wata makala dake cewa, jam’iyyar Republican ta Amurka, na sake rubuta tsohon tarihin ta na dorawa wasu kasashe laifin yaduwar cuta, bayan gazawar ta a fannin yaki da cutar a cikin gida.

Tsokacin Washington Post na zuwa ne, bayan da ita ma jaridar “South China Morning Post” ta yankin Hong Kong ta bayyana cewa, daga makwanni kadan baya, nau’in cutar COVID-19 na delta ya bulla a lardin Guangdong na kasar Sin, amma managartan matakan kandagarki da aka dauka sun haifar da nasarar dakile cutar ba tare da kashe tarin kudade ba.

Kaza lika jaridar ta ce, idan har ana iya rage bazuwar cutar bayan bullar ta, hakan na tabbatar da cewa za a kai ga cimma nasarar kakkabe ta, ba tare da bata lokaci ba. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version