Jarimi Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa 750 A Kaduna

Jarimi

Daga Ibrahim Ibrahim,

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta kudu, wanda kuma a halin yanzu shi ne Dan takarar kujerar Shugabancin Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a karo na biyu, Honarabul Kabir Yakubu Jarimi ya tallafawa Mata da Matasa har su kimanin dari 750 masu Kananan sana’o’i da zunzurutun kudi sama da naira miliyan sha daya da dubu dari biyu 11.2, domin su dogara da Kansu.

Honarabul Jarimin yace ya bayar da wannan tallafin kudi ne domin wanda aka tallafawa su inganta sana’o’insu da kuma kara dogaro da kansu.

Ya kara da bayyana cewa, yin hakan zai dauke hankulan musamman Matasan daga miyagun halaye kamar su shaye shaye da wasu ayyukan ta’addanci wanda zai iya kaisu ga fadawa ga halaka.

A fadarsa, wannan shi ne babban tallafi da wani Dan siyasa a matakin karamar hukuma ya taba bawa masu kananan sana’o’i.

Jarimi wanda shi ne ke sake takarar naiman kujerar Karamar hukumar Kaduna ta kudu ya ce, wannan adadin namba ta dari bakwai da hamsin 750 na wadanda zasu amfana da tallafin an zakulo su ne daga Gundumomi goma sha uku 13 dake cikin Karamar hukumar Kaduna ta kud, kuma kowanne mutum zai sami dubu goma sha biyar 15000 domin kara bunkasa Sana’arsa.

A cewarsa, “Burina shi ne na ga duk wani mai karamar Sana’a ya tsaya da kafarsa, sannan ina matukar son ganin na kawar da Talauci ta hanyar samar da ayyukan yi ga Mata da Matasanmu.”

“Ko da ina kan kujerar mulki ko bana kai, mutane na suna cikin zuciyata, saboda a ko da yaushe nakan tuna halaccin da kukayi min a lokacin da nake kan kujerar Shugabancin karamar hukumar kaduna ta kudu, da wannan nake kara naiman marawar bayanku a karo na biyu a zabe na gaba domin ci gaba daga inda muka tsaya.”

Tsohon Shugaban Karamar hukumar ya janyo hankalin wadanda suka amfana da tallafin kan cewar su yi amfani da abin da suka samu ta hanya me kyau wanda zasu Mora nan gaba.

Shima a nasa bayanin, Shugaban Jam’iyyar APC a matakin Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Honarabul Yakubu Soso, ya nuna farin cikinsa game da wannan tallafi tare da janyo hankalinsu ganin cewa sunyi amfani da kudin ta hanyar da ya kamata.

Honarabul Soso ya yi kira ga daukacin Mutanen Karamar hukumar Kaduna ta kudu kan cewa a zabe mai zuwa, su tabbatar sun fito gaba dayansu domin sake zaben Jam’iyyar ta APC, tun daga matakin Kansiloli har zuwa na Shugaban Karamar Hukuma. A cewarsa.

Exit mobile version