Jarin Da Sin Ta Zuba A Kasashen Da Suka Ratsa Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Daga Janairu Zuwa Mayu Ya Karu Zuwa Kaso 13.8

Daga CRI Hausa

Alkaluman da ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta fitar Alhamis din nan na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Mayun wannan shekara, jarin kai tsaye da bai shafi harkokin kudi ba da kasar Sin ta zuba a ketare, ya kai Yuan biliyan 280.62, daga cikin jarin kai tsaye da bai shafi harkokin kudi ba da kasar Sin ta zuba a kasashen dake hanyar shawarar ziri daya da hanya, ya kai dalar Amurka biliyan 7.43, karuwar kaso 13.8 kan na shekarar da ta gabata.

Alkaluma na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Mayu, jarin kai tsare na ketare da kasar Sin ta yi amfani da shi, ya kai Yuan biliyan 481, karuwar kaso 35.4 cikin 100 kan shekarar da ta gabata.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

Exit mobile version