Mukhtar Yakubu" />

Jarumai 10 Da Tararuwar Su Ta Haska A 2020

Kusan a kowacce rana ta Allah daga safiya zuwa yamma, babu wata rana da za ta fito ta fada ba tare da an samu ko da mutum daya ya shigo masana’antar finafinai ta Kannywood, wannan ya a ke yi wa masana’antar kallon wata kasuwar da babu wadda ta kai ta girma a kasar Hausa domin kuwa masana’anta ce da a harkar kasuwancin da babu iyaka a cikin ta, don haka duk yadda mutum ya shigo to zai samu wajen zama a cikin ta.

Sai dai kusan duk mafi yawan mutanen da su ke shigowa cikin masana’antar finafinai ta Kannywood, kowa yana zuwa ne da niyyar ya zama babban jarumi. Wannan dabi’a ta zama babban jarumi kowa haka ya ke da burin ta mata da maza, to sai dai a cikin Jarumai dubu da za su shigo harkar, yana da hawala ka samu guda 20 sun zama jaruman da duniya ta san su, saboda daukaka ta Allah ce, domin ko a shekarar 2020 da ta gabata, duk da masana’antar ta finafinai ta yi kasa, to hakan bai Hana dumbun jama’a maza da mata kwararowa cikin masana’antar ba, Amma duk da haka an samu wasu daga cikin su da suka haska duniya ta san su. Wasu Sabbin fuska ne ba a san da su ba sai a shekarar ta, 2020, wasu kuma sanannu ne da harkar ta ajiye su, sai a shekarar 2020 din suka kara haskawa, don haka suka shiga cikin fitattun jaruman da suka haska a shekarar ta 2020, kamar yadda za mu kawo nazarin da muka yi muka fitar da jarumai 10 da suka haska don haka sai ku biyo mu a cikin nazarin.

1 NAFISA ABDULLAHI

Nafisa Abdullahi. Sumayya a Labarana

Jaruma Nafisa Abdullahi ta dade tana haskawa a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood, sai dai ta kwanta tsawon lokaci ba a jin labarin ta, sai a wannan shekarar da aka fara haska fim din Labarana mai dogon Zango a tashar Arewa 24, kasancewar ita ce jarumar fim din, da kuma irin rawar da ta ke takawa a matsayin Sumayya ya sa ta shiga sahun fitattun jarumai da suka haska a shekarar 2020.

2 FATIMA KINAL

Fatima Kinal

Wannan sabuwar jaruma ce da ba a taba saka ta a cikin fim ba sai a shekarar 2020, amma fim din ta da ta fito a matsayin jarumar fim din da sunan Fati wanda Abubakar Bashir Maishadda ya dauki nauyin sa ya sa ta shiga cikin Jaruman da suka haska a shekarar 2020, domin tun da aka haska fim din a film House da ke Shoprate a Kano sai jarumar ta zama tauraruwa.

3 HAUWA AYAWA AZIMAR GIDAN BADAMASI

Hauwa Ayawa, Azimar Gidan Badamasi

Ita ma sabuwar jaruma ce da ba a san fuskar ta ba sai a shekarar 2020. Amma fara ganin ta a cikin fim mai dogon Zango na Gidan Badamasi, da a ke haskawa a tashar Arewa 24, da irin rawar da ta ke takawa ya sa da zama fitacciyar jaruma a shekarar 2020.

4 ABDULLAHI DAN’AZUMI AMDAZ. EXCELLENCY.

Abdullahi Amdaz, Excelency a Labarina

Ya kasance jarumi mawaki kuma marubucin labarin fim. Amma a shekarar 2020 ya kasance cikin fitattun jarumai saboda irin rawar da ya taka a cikin fim din Labarina, a matsayin Edcellency, don haka a yanzu dai in ba ka Kira shi da Edcellency ba, to ba ma za a gane shi ba saboda ya zama fitaccen jarumi a 2020 da sunan Edcellency.

5 AISHA NAJAMU

Ita ma sabuwar jaruma ce da ba a san ta ba sai a shekarar 2020. Amma fim din Izzar So na kamfanin Bakori da a ke sakawa a shafin sa na You Tube ya sa ta zama cikin jarumai da suka zama fitattu a shekarar 2020. Ba kuma wani abu ya ja hankalin mutane ba a kan ta sai irin rol din da ta taka in da ta zama mai nuna Isa da iko a cikin fim din.

6 KHADIJA YOBE

Khadeejah Yobe

Sabuwar jaruma Khadija Yobe, ta tsinci Damen ta a kale cikin shekarar 2020, domin babu wanda ya san ta, a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood. Amma fitowar da ta rinka yi a cikin fim din Izzar so ya mayar da ita fitacciyar Jaruma a 2020.

7 LAWAN AHMAD

Lawan Ahmed

Ya dade yana Jan zaren sa a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood, amma duk tsawon shekarun da ya shafe sama da 15 bai samu damar da duniya ta san shi ba har a ke yi masa kallon babban jarumi ba sai a shekarar 2020, saboda kasancewar sa jarumin da ya ja fim din Izzar so.

8 NUHU ABDULLAHI

Nuhu Abdullahi, Mahmoud a Labarina

Ya kasance a matsayin Mahmoud a cikin shirin Labarana, kuma sunan da ya yi fice da shi kenan a shekarar 2020. Duk da kasancewar sa tsohon Jarumi, amma bai taba samun suna da daukaka ba kamar a shekarar 2020, da sunan Mahmoud a fim Labarana, don haka yana cikin Jaruman da sunan su ya yi fice a masana’antar finafinai ta Kannywood a 2020, din da ta gabata.

9 SANI MU’AZU Bawa Mai kada

Sani Mu’azu, Bawa Maikada a kwana Casa’in

Masu kallo a shekarar 2020 ba za su manta da Sani Ma’azu, ko kuma Bawa Maikada na cikin Kwana Casa’in ba, domin rol din da ya taka a cikin shirin ya samu karbuwa sosai a wajen masu kallo, don haka ya zama fitaccen jarumi a shekarar 2020.

10 RAYYA

Surayya Aminu, Rayya Kwana Casa’in

Ita ma fa Rayya ta cikin Kwana Casa’in, ta haska a cikin shekarar 2020, domin kuwa tana cikin Jaruman da masu kallon shirin Kwana Casa’in, suka fi so su gani, don haka ta zamo cikin fitattun jarumai da suka haska a shekarar 2020.

 

Exit mobile version