Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Jarumar Da Ta Fi Ko Wacce Tsawo A Tarihin Nollywood

Ko kun san cewa jaruma Stephanie Okereke Linus ita ce jarumar da ta fi ko wacce tsawo a tarihin kafuwar masana’antar fina-finan da ake yi a kudancin kasar nan ta Nollywood?

Jarumar kuma har ila yau daraktar fim ta yi sana’ar tallata kayan ado kafin ta tsunduma cikin fim gadan-gadan.

Ta taba shiga gasar Sarauniyar Kyau ta Nijeriya inda ta kai zagaye na karshe a shekarar 2002.

Bayan nan ne ta mayar da hankali a kan harkar fim kacokaf, inda bayan shekara biyu aka gabatar da sunanta sau takwas don lashe gasar kyaututtuka ta jaruman fim. Ta sami lambobin yabo sau biyu a fagen fim, kana an ba ta lambar yabo ta kasa ta OFR. Ita ce har ila yau, ta shirya fina-finan turanci masu sunan “Through the glass” da kuma “Dry”.

Manazarta dai sun ce kasancewarta mace sambaleliya da kyan fuska duk irin tufafin da ta saka suna ma ta kyau matuka wanda hakan ke birge masoyanta na nesa da kusa.

Stephanie ta yi aure tun a shekarar 2012 tare da masoyinta Linus Idahosa a Birnin Faris na Kasar Faransa.

Exit mobile version